Jagoran PDP Ya Fadi Gwamnan PDP da ya yi Silar Sauya-Shekar Kwankwaso Zuwa NNPP

Jagoran PDP Ya Fadi Gwamnan PDP da ya yi Silar Sauya-Shekar Kwankwaso Zuwa NNPP

  • Mohammed Jamu ya bayyana abin da ya jawo Rabiu Musa Kwankwaso ya zabi ya kawo karshen zamansa a PDP
  • A cewar Jamu, hana shi zama mataimakin shugaban jam’iyya ya fusata Kwankwaso, ya koma jam’iyyar NNPP
  • ‘Dan siyasar yana zargin Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal ya taka rawar gani wajen rasa tsohon mai gidan na sa

Kano - Mohammed Jamu ne wanda bangaren Rabiu Musa Kwankwaso suka so ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Arewa maso yamma.

Sai dai wasu jiga-jigan jam’iyyar ba su yarda Mohammed Jamu ya rike kujerar ba, an ji a dalilin wannan tsohon gwamnan na Kano ya yi watsi da PDP.

Mohammed Jamu ya yi hira da gidan talabijin na Trust TV, ya yi bayanin yadda wannan rikicin cikin gida ya jawo PDP tayi asarar Sanata Kwankwaso.

Kara karanta wannan

2023: Babban Dalilin da Yasa Na Ɓoye Manufofina Ga Yan Najeriya, Kwankwaso Ya Magantu

‘Dan siyasar yace bai san da batun takarar shugabancin ba sai daf da lokacin zabe, ya shirya ya wuce Kaduna, amma sai wasu suka hana ayi zaben a lokacin.

Sai ga kiran waya daga Rabiu Musa Kwankwaso,

Na ji kiran waya daga Dr Rabiu Musa Kwankwaso, yana sanar da ni cewa shugabannin PDP a Kano sun zabe ni in zama mataimaki shugaban jam’iyya na Arewa maso yamma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin ya ba ni mamaki, ya girgiza ni.
Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso da manyan NNPP Hoto: @Ibraheemz01
Asali: Facebook
Daga nan na fara shiri domin saura kwanaki biyu ayi zabe. Ya kamata a ce muna Kaduna a ranar Asabar, amma sai Laraba aka sanar da ni, na shirya na tafi Kaduna washegari.
Daga lokacin har zuwa Mayun shekarar nan, an yi ta yi gaba ana baya. Sau uku ana shiryawa za ayi zaben, sai wani abin ya hana, kan wannan Kwankwaso ya zabi ya bar Jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

2023: Babban Jigon PDP Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi, Ya Koma Jam’iyyar LP

Rawar Aminu Waziri Tambuwal ya taka

Bakanon yace watakila Aminu Waziri Tambuwal ya ji tsoron yana neman zama shugaban kasa, kuma Kwankwaso mai shirin takara zai iya kawo masa cikas.

A matsayinsa na shugaban gwamnonin PDP a lokacin Uche Secondus, Jamo ya fadawa jaridar cewa fam daya gwamnan na Sokoto ya bada umarnin a saida.

A karshe Jamu ya samu fam din shiga takara, amma yace ko a lokacin da aka je yin zabe a Kaduna, Kwankwaso ya fice daga PDP, yana ganin ba a mutunta shi ba.

Rikicin PDP: Dole ayi gyara - Jamu

A hirar da aka yi da shi, Jamo yace sakacin Iyorchia Ayu ya jawo suka rasa Kwankwaso, Peter Obi, sannan yanzu Gwamna Nyesom Wike ya janye gindinsa.

Kamar yadda Jamu ya yi bayani, ya kamata PDP ta kawo karshen rigingimun cikin gidanta.

Mutum 13, 000 sun shiga PDP

A makon nan aka ji labarin Jam’iyyar APC tana cigaba da yin rashi a Katsina tun da tsohon SSG, Mustapha Muhammad Inuwa da mutanensa suka bi PDP mai adawa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso @66: Wasu abubuwa 10 da ba ka sani ba a game da ‘Dan Takaran NNPP

Yakubu Lado Danmarke ya karbi dubunnan mabiya da shugabannin jam’iyyun APC mai mulki da NNPP mai kayan dadi da suka sauya-sheka daga Jibiya da Kaita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng