Jerin Abubuwa 10 da Bola Tinubu Ya yi wa ‘Yan Najeriya Alkawari a Manufofinsa

Jerin Abubuwa 10 da Bola Tinubu Ya yi wa ‘Yan Najeriya Alkawari a Manufofinsa

  • A yau ‘dan takarar shugaban kasana jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fitar da takardar manufofinsa mai tsawon shafuka har 80
  • Punch ta bi jerin alkawuran da Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya domin su zabe shi.
  • Jerin alkawuran sun shafi sha’anin tsaro, yadda za a bunkasa tattalin arziki, gyare-gyaren da za a kawo a bangaren mai da bangaren ilmi

Alkawura 10 da Bola Tinubu ya yi

1. Gina Najeriyar da matasa za su samu ayyukan yi tare da albashi mai tsoka domin jin dadin rayuwa.

2. Samar da kaya da ayyukan da ake bukata. Najeriya za ta rika samar da arziki, a maimakon kasancewa ci-ma-zaune.

3. A rika fita da arziki daga Najeriya, a rage yawan kayan da ake shigowa da su daga kasashen ketare.

4. Cigaba da taimakawa manoma ta hanyar tsare-tsaren aikin gona da za su sa al’umma ta koshi da abinci.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya fadi babban sauyin da zai kawo a aikin 'yan sanda idan ya gaji Buhari

5. Zamanantar da abubuwan more rayuwa ta yadda tattalin arzikin kasa zai cigaba daidai gwargwado.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

6. Tallafawa matasa a bangarori masu tasowa irinsu tattalin arzikin zamani, nishadi, al’adu da yawan bude ido.

7. Rage talauci ta hanyar horas da jama’a ta yadda za su samu arziki domin yara su daina kwana da yunwa.

8. A raba wutar lantarki domin mutane su samu haske wajen gudanar da ayyukansu da jin dadin zama a gida.

9. Kawo tsare-tsaren da za su taimaka wajen ganin kiwon lafiya, ilmin zamani da mallakar gidaje bai gagara ba.

10. A fito da tsare-tsare na musamman da za su kawo karshen ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran ta’adi.

Babu ruwa na da yi wa APC kamfe

An ji labari Fasto Gideon Para-Mallam yace ba zai yi wa APC kamfe domin ba a nemi izininsa ba, kuma bai goyon bayan tikitin Musulmi-Musulmi.

Para-Mallam ya nuna shi ba ‘dan siyasa ba ne, duk da yana ganin shiga jam’iyya ba laifi ba ne, sai dai a irin wannan lokaci, bai da ra’ayin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel