Kwankwaso: Manyan Arewa na Shirin Goyon Bayan Wani ‘Dan Takara ‘Mara Shahara’

Kwankwaso: Manyan Arewa na Shirin Goyon Bayan Wani ‘Dan Takara ‘Mara Shahara’

  • Rabiu Musa Kwankwaso ba zai halarci taron da kwamitin manyan Arewa suka kira ‘yan takara ba
  • ‘Dan takarar shugabancin na Najeriya ya zargi kwamitin da neman fifita wani ‘dan takara a zaben 2023
  • Sanata Kwankwaso mai neman a mulki jam’iyyar NNPP ya yi kira ga manyan yankin su guji son kai

Kaduna - ‘Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan zaman su da kwamitin shugabannin Arewa.

Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi wasu daga cikin ‘yan kwamitin da niyyar tsaida wani ‘dan takara. Abdulmumin Jibrin ya bayyana wannan a wata sanarwa.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan na NNPP, Hon. Jibrin ne ya fitar da jawabi a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba 2022.

Kara karanta wannan

Yadda Zan Tsaya Na Yaki Yan Bindiga Idan Na Zama Shugaban Kasa a 2023, Tinubu

An rubuta takardar a ranar Juma’a da ta gabata, amma a yau ta shigo hannun Legit.ng Hausa. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a yammacin yau.

Tsohon gwamnan na Kano ba zai je gaban wannan kwamiti da zai tantance ‘yan takaran shugaban kasa domin su fadawa 'Yan Arewa wanda za su zaba ba.

Magoya bayan NNPP
Wasu Magoya bayan Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHassan
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Kakakin kamfen na NNPP

“Muna da bayanai masu karfi a wajenmu da ke nuna cewa wasu mutane sun kammala shirin maida tsarin wata damar tallata wani ‘dan takara.
Mun yi imani cewa ba daidai ba ne wasu mutane ko wata kungiya ta goyi bayan wani ‘dan takara ta bayan-fage da sunan yankin Arewacin Najeriya.
Musamman a lokacin da muke da ‘yan takara fiye da daya daga yankin na Arewacin Najeriya.
Saboda haka muna ba ku shawarar ku gujewa wani abin da zai bata sunan Ahmadu Bello da sauran manyan Arewa irinsu Tafawa Balewa, Aminu Kano, Sir Kashim Ibrahim da J.S. Takra, ta hanyar goyon bayan ‘dan takaran da bai shahara ba, a maimakon wanda ya fi shahara, ya fi sanin aiki, ya fi nagarta.

Kara karanta wannan

Sunan Darektan Kamfe a APC Ya Fito a Kwamitin Yakin Neman Zaben Peter Obi

Hadimin na Kwankwaso ya kara da cewa ya san yadda zai magance matsalolin da ke damun Najeriya, kuma ya yi wannan bayani a cikin manufofinsa.

‘Dan siyasar yace zai fito da takardar da zarar an kammala aikinsa wanda zai magance matsalar noma, rashin aikin yi, shaye-shaye da sauransu.

Kuri'u miliyan 5 a Kano

Hon. Abdulmumuni Jibrin mai neman takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Kiru/Bebeji yana sa ran NNPP za tayi nasara a zaben 2023.

An ji labari Hon. Abdulmumuni Jibrin ya yi alkawari Rabiu Musa Kwankwaso zai samu kuri’u miliyan 5 a Kano ta hanyar shiga duk wani lungu da sako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel