Atiku Ne Ya Bani Shawaran In Karbi N1bn Amma Na Ki, Iyorchia Ayu

Atiku Ne Ya Bani Shawaran In Karbi N1bn Amma Na Ki, Iyorchia Ayu

  • Iyorchia Ayu ya bayyana yadda hakayi kan zargin da Wike ke masa na karban kudi N1billion
  • Ayu ya ce dalilin da yasa yaki mayarwa Wike martani shine saboda kawai a zauna lafiya a jam'iyyar
  • Nyesom Wike Ya lashi takobin sai Ayu ya sauka, Shi kuwa Ayu yace lallai zabensa akayi ba zai sauka ba

Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party, Senator Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa dan takarasu Atiku Abubakar ya bashi shawarar karban bashin N1bn amma ya ki.

Ya bayyana hakan ne yayin martani ga Wike wanda ya zargesa da karban N1bn daga wajen wani gwamna.

Ayu ya bayyana cewa tun lokacin da ya hau kujerar ya tarar jam'iyyar bata da kudi amma duk da haka bai karbi ko sisi hannun wani ba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Wike Yace Ba Atiku Kadai Bane Dan Takarar PDP

Yace har shawara Alhaji Atiku Abubakar ya bashi ya karbi bashin N1bn.

Atiku
Atiku Ne Ya Bani Shawaran In Karbi N1bn Amma Na Ki, Iyorchia Ayu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike a ranar Juma'a ya tsokano shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, kan zargin almundahanar da yayi masa a watan Satumba.

Wike ya kara yanzu da cewa Ayu fa ya karbi milyan dari hannun wani gwamna, sannan ya koma wajen kwamitin gudanarwa ya sake karban wani milyan dari.

Wike ya bayyana hakan yayin hira da yan jaridar ranar Juma'a a birnin Port Harcourt.

Ayu yace:

"Lokacin da ya fara zargi na cewa na karbi N1billion. Na ki bashi amsa ne saboda ba son tada tarzoma a jam'iyyar. Amma bari in fayyace cewa ko sau guda ban karbi N1bn hannun kowa ba."
"Kuma N100m da wani gwamna ya bada gudunmuwa mun yi amfani da shi wajen aikin da akayi niyyar yi. Nan da yan makonni zamu gayyaci jigogin jam'iyya har da yan jarida don kaddamar da PDI."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ayu Yayi Martani Kan Zarginsa da Wike Yayi na Cin Rashawar N100m da N1b

"Lokacin da muka shigo jam'iyyar na fuskantar matsalar kudi, dan takaranmu ya bani shawarar in karbi bashin N1bn daga wajen banki."
"Amma da muka tattauna na, muka fasa hakan. Bamu karbi bashi hannun kowa ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel