2023: Wanda Atiku Ya ba Mukami, Ya Watsa Masa Kasa a Ido, Yace Ba Zai Karba ba

2023: Wanda Atiku Ya ba Mukami, Ya Watsa Masa Kasa a Ido, Yace Ba Zai Karba ba

  • Dr. Sam Amadi yace ba zai karbi tayin mukamin Darekta a kwamitin yakin neman zaben PDP ba
  • Masanin ya tabbatar da haka a wata takarda da ya aikawa Gwamna Aminu Waziru Tambuwal
  • Amadi yake cewa wuraren da yake aiki ba za su ba shi dama ya shiga harkar siyasa tsamo-tsamo ba

Abuja - Fitaccen masanin nan, Dr. Sam Amadi ya yi watsi da tayin kujerar Darekta a kwamitin zaben shugaban kasa da Atiku Abubakar ya yi masa.

Rahoton The Cable yace Darektan na makarantar Abuja School of Social and Political Thoughts ya gabatar da uzurinsa na kin karbar wannan mukami.

Dr. Sami Amadi yace ya ki karbar aikin Darektan bincike na kwamitin neman jam’iyyar PDP a 2023 ne saboda yanayin irin ayyukan da yake yi.

Kara karanta wannan

Da Sauran Aiki: Sanatar PDP Ta Gano Katuwar Matsala a Cikin Kasafin Kudin 2023

Amadi yake cewa aikin da yake yi bai ba shi damar da zai fito ya nuna ra’ayin siyasar da yake yi ba, yace ana bukatar ya zama bai da sheka a siyasance.

Rahoton yace Amadi ya yi wannan bayani a wata wasika da ya rubuta a ranar Litinin, ya aikawa Darekta Janar na kwamitin, Aminu Tambuwal.

Wasikar Dr. Sami Amadi

“Da farko ina mai godiya sosai da aka yi mani tayin Darektan bincike na kwamitin yakin neman zaben shugaban kas ana PDP a zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ifeanyi Okowa Hoto: @IAOkowa
Ifeanyi Okowa, Iyorchia Ayu da Emeka Ihedioha Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter
Na dauki wannan a matsayin wani gagarumin abin alfahari, a ga cancanta da in rike wannan babban ofis a kwamitin takarar shugabancin kasa.
Ina farin cikin cewa kwamitin yana karkashin jagorancin mutum mai daraja da kima, wanda nake alfaharin yin aiki da shi a lokutan baya.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

Nagode, sai dai kash ... - Amadi

“Amma duk da karrama ni da aka yi a matsayin daya daga cikin darektocin da za suyi aiki da ku, ina so in ki karbar wannan mukami, in gujewa matsayin.
Dalilin kin amincewa da mukamin shi ne za a samu daga aikin da nake yi, ina jagorantar jama’a da-dama, ana bukatar in zama babu ruwa na da ra’ayin siyasa.

A cewar Amadi, yana aiki da makarantar ASSPT, kungiyar CAN da gidan talabijin Arise TV wanda duk ba a bukatar ya zama yana tare da wata jam’iyya.

Dailypost tace an yi wa takardar take “Kin karbar aikin Darekta na bincike a kwamitin PCC na PDP.”

A karshe yace matsayarsa bai nufin rashin goyon bayan jam'iyyar PDP ko 'dan takararta watau Atiku Abubakar a babban zaben da za ayi a 2023.

Lafiyar Tinubu kalau?

A baya kun ji labari Sanatan yammacin Enugu, Chimaroke Nnamani ya fito fili yana yabon Bola Tinubu duk da yace Atiku Abubakar ne ‘dan takararsa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Sanata Nnamani ya tabbatar da cewa ya zauna da ‘dan takaran APC, kuma ya same shi cikin cikakken koshin lafiya, akasin rade-radin da suke yawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel