Jiragen sama 15 Sun Sauka Yayin da Atiku Ya Kaddamar da Kamfen 2023

Jiragen sama 15 Sun Sauka Yayin da Atiku Ya Kaddamar da Kamfen 2023

  • Jirage barkatai sun sauka a babban filin jirgin saman Victor Attah da ke garin Uyo a farkon makon nan
  • Gwamnoni da sauran manyan jam’iyyar PDP sun je Akwa Ibom domin kaddamar da yakin neman zabe
  • Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa sun fara neman mulkin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP

Akwa Ibom - Rahoton da Punch ta fitar a farkon makon nan ya nuna yadda jam’iyyar PDP mai neman mulkin Najeriya ta fara yakin neman zabenta na 2023.

Ana maganar akalla jiragen sama 15 suka sauka a babban filin sauka da tashin jiragen sama na garin Uyo a jihar Akwa Ibom a ranar Litinin domin kamfe.

Gwamnonin jam’iyyar PDP da aka gani a wajen kaddamar da kamfe din sun kunshi Aminu Waziri Tambuwal wanda shi ne Darekta Janar na yakin zabe.

Sai kuma Ahmadu Umaru Fintri na jihar Adamawa, Darius Ishaku na Taraba; da Mai girma Gwamna Udom Emmanuel wanda shi ne mai masaukin baki.

Sauran gwamnonin da aka gani su ne: Gwamnan Bayelsa, Douye Diri; Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed; Gwamnan Edo, Godwin Obaseki; da Ifeanyi Okowa.

Wasu Gwamnoni sun ki zuwa

Akwai wasu gwamnonin jihohin PDP da suka kauracewa taron da jam’iyyarsu ta shirya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin nan sun hada da Nyesom Wike da wadanda suke bangarensa irinsu Seyi Makinde, Samuel Ortom, Ikpeazu Okezie da kuma Ifeanyi Ugwuanyi.

Atiku
Atiku Abubakar a Uyo Hoto: @Atikuorg
Asali: Facebook

Jiragen sama a Akwa Ibom

Jaridar tace jiragen da aka gani a babban filin jirgin tashin Victor Attah sun hada da Hawker Siddeley 125 mai lamba 5N-BZP na kamfanin Jubilee Aviation.

An ga jirgin saman Jed Air na Bombardier Challenger 604 mai lamba 5N-BYN, sai jirgin HS 125 mai lamba 5N-BZT da wani jirgin Embraer Phenom 300 (E55P).

Sauran wadanda aka iya hange su ne: Jirgin Dogon Daji kirar HS125 mai lamba 5N-BNM da Lear Jet 45 mai dauke da lamba 5N-BLW da jirgin Embraer E135.

Wani jirgin saman da ya sauka a Uyo jiya shi ne Embraer E145 da wani jirgin Embraer E135 dabam, sai jirgin Embraer E145 daga United Nigeria Airlines.

Ba a ga jirgin saman Atiku Abubakar kirar Global Express a filin ba, haka zalika ‘yan jarida ba su hango jirgin saman jirgin Akwa Ibom mai lamba N224BV ba.

Tinubu bai da rashin lafiya - Chimaroke Nnamani

Dazu kun ji labari Sanatan yammacin Enugu, Chimaroke Nnamani ya fito fili yana yabon Bola Tinubu duk da kuwa yace Atiku Abubakar ne ‘dan takararsa a 2023.

Sanata Chimaroke Nnamani ya tabbatar da cewa ya zauna da ‘dan takaran APC, kuma ya same shi cikin cikakken koshin lafiya, akasin rade-radin da ke yawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel