Yayin da Aka Hana APC Shiga Takara a Akwa Ibom, Kwankwaso Ya Ci Kasuwa a Jihar

Yayin da Aka Hana APC Shiga Takara a Akwa Ibom, Kwankwaso Ya Ci Kasuwa a Jihar

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da sakatariya da ofishin kamfe na NNPP a Akwa Ibom
  • An yi dan karamin biki wajen tarbar ‘Dan takaran Shugaban kasar da ‘yan tawagarsa a garin Uyo
  • Tsohon jigo a APC, Sanata John Akpanudoedehe shi ne yake yi wa NNPP takarar Gwamna a Akwa Ibom

Akwa Ibom - Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a karkashin NNPP ya shiga jihar Akwa Ibom a yammacin Alhamis.

A wani jawabi da ya shigo hannun Legit.ng Hausa, mun ji jirgin yakin neman zaben Rabiu Kwankwaso ya sake lekawa Kudu maso kudancin Najeriya.

Saifullahi Hassan a sanarwar da ya bada, yace ‘dan takaran shugaban kasar ya kaddamar da babban ofishin yakin neman zaben NNPP da ke jihar.

Ofishin neman takaran jam’iyyar ta NNPP a 2023 yana nan a hanyar Edet Akpan a garin Uyo.

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Atiku Abubakar a PDP Ya Samu Mukami a Kwamitin Neman Zabensa

Baya ga sakatariyar jam’iyya na jiha, Sanata Rabiu Kwankwaso ya bude wasu ofisoshin takarar Hon. Abasiamanam Effiong da na Hon. Kufre Eshiet.

Effiong da Eshiet suna neman takarar majalisar tarayya a inuwar NNPP. Legit.ng Hausa ta fahimci ofishin ‘yan takaran suna garuruwan Ibiono Udom da Uyo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwankwaso
Magoya bayan Kwankwaso da NNPP a Akwa Ibom Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Mutane da-dama da ke goyon bayan jam’iyyar hamayya ta NNPP da kuma masoya jagoran na darikar siyasar Kwankwasiyya suka halarci wannan taro a jiya.

Kaddamar da hedikwatar da ke garin Uyo na zuwa ne a lokacin da ake shirye-shiryen karasa aikin babban ofishin yakin neman zaben NNPP a garin Abuja.

Taro ya zama biki - Kwankwaso

Da yake magana a shafinsa na Twitter, ‘dan takaran yace zuwansa Akwa Ibom ya zama biki. An ga ‘dan siyasar tare da irinsu Sanata John Akpanudoedehe.

“Yau biki aka yi da na sauka a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom domin kaddamar da babbar hedikwatar @OfficialNNPPng na jihar.

Kara karanta wannan

Na Hannun Daman Dankwanbo da Wasu Jiga-Jigan PDP 4 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Gombe

Na godewa mutanen kasar alkawari da irin soyayya da goyon baya da suka nuna mana. #NewNigeria" - Rabiu Musa Kwankwaso.

Kawancen APC da NNPP

Kwanakin baya kun ji labari cewa wasu jiga-jigan APC na reshen jihar Akwa Ibom, sun ce za su karbi John Akpanudoedehe a matsayin ‘dan takaransu a 2023.

Tsohon sakataren APC na kasa shi ne yake yi wa NNPP takarar Gwamna a Akwa Ibom, ita kuma jam’iyyar APC ba ta da ‘dan takara saboda rikicin cikin gida.

-

Asali: Legit.ng

Online view pixel