Ba Zai Yuwu Mu sha Kaye a 2023 Ba: Aisha Buhari Tayi Muhimmiyar Ganawa da Matar Tinubu

Ba Zai Yuwu Mu sha Kaye a 2023 Ba: Aisha Buhari Tayi Muhimmiyar Ganawa da Matar Tinubu

  • Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da matar ‘dan takarar shugaban kasa na APC, Remi Tinubu da matan gwamnonin APC sun gana a Abuja
  • Taron da suka yi sun yi ne domin tsara yadda jam’iyyar da ‘dan takararta zasu lashe zaben 2023 mai gabatowa
  • Uwargidan Buhari tayi kira ga matan APC da su dage da duk iyawarsu wajen ganin an ci zaben don tace ba zasu iya zuba ido a lallasa su ba a 2023

FCT, Abuja - Uwargidan shugaban kasan Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari tare da matar ‘dan takarar shugabancin kasa na APC, Sanata Oluremi Tinubu suna yi wata ganawa mai muhimmanci a ranar Lahadi, 9 ga wata Oktoba.

Aisha Buhari
Ba Zai Yuwu Mu sha Kaye a 2023: Aisha Buhari Tayi Muhimmiyar Ganawa da Matar Tinubu. Hoto daga Presidency
Asali: Facebook

Taron ya samu halartar mata mambobin jam’iyyar APC da matasan tawagar kamfen din kujerar shugabancin kasan kuma an yi shi ne a gidan gwamnati dake Abuja, jaridar PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Amaechi, da ‘Yan APC 10 da Suka Nemi Takaran 2023, Amma Aka Daina Jin Duriyarsu

Sauran fitattun matan da suka samu halartar taron sun hada da matar ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, Nana Shettima, darakta janar ta cibiyar ga aka mata ta kasa, Asabe Velita-Bashir da matan gwamnonin APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Uwargidan shugaban kasan wacce ita ce shugabar tawagar kamfen na mata na jam’iyyar, tayi kira da hadin kai tare da aiki tare wurin tabbatar da APC ta lashe zaben a 2023.

“Ya zama dole matan APC su hada kansuwa domin samar da karfin goyon baya da tabbatar da nasara a jam’iyyar yayin zaben dake gabatowa.”

Kamar yadda tace, jam’iyyar ba zata zuba ido ta fadi zabe mai zuwa ba. Ta bayyana cewa, nasarar da APC ta samu a shekarar 2015 da 2019 ta biyo bayan hadin kansu ne.

Uwargidan shugaban kasan ta kara da cewa:

“Ba zamu iya zuba ido mu fadi ba amma zamu yi aiki tare da dunkulewa wuri daya domin samun nasara a zaben 2023. APC ta zabi ‘yan takararta na dukkan kujerun mika an siyasa kuma yanzu ne lokacin da zamu farfado da gangamin mu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel