Jerin Gwamnonin Da Ke Naman Tazarce Zuwa Wa'adi Na Biyu Na Mulki A Zaben 2023

Jerin Gwamnonin Da Ke Naman Tazarce Zuwa Wa'adi Na Biyu Na Mulki A Zaben 2023

  • Akalla gwamnoni 11 dake kan karagar mulki ne a Najeriya ke neman tazarce a zaben gwamnan da za a yi a 2023
  • Wasu daga cikin gwamnonin dai akwai yiwuwar su iya nasarar tazarce ba tare da wata matsala ko tsaiko ba
  • Wasu gwamnonin jihohin kuwa, na iya fuskantar kalubale daban-daban gabanin zaben wanda ka iya taba damarsu ta tazarce

Yayin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saki sunayen 'yan takarar gwamna 28 a Najeriya da za su gwabza a zaben 2023, 11 daga cikinsu na neman wa'adi na biyu ne.

A cewar wani rahoton The Nation, an saki wannan jerin sunaye ne a jiya Laraba 5 ga watan oktoba, kuma shine jerin 'yan takara na karshe da INEC ta amince dashi.

Kara karanta wannan

Fushin Gwamnoni: Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Gwamnoni 11 dake neman tazarce
Zaben 2023: Jerin Gwamnonin Da Ke Naman Tazarce Zuwa Wa'adi Na Biyu Na Mulki | Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Alamu na nuna akwai gwamnonin da za su samu saukin tazarce a zaben mai zuwa, wasu kuwa na da alamar shan fama kafin iya komawa a wa'adi na biyu.

Hakazalika, jerin ya nuna cewa, jam'iyyun siyasa 18 a jihohi 28 sun mika sunayen 'yan takarar gwamna 837 da za su yi takara a 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, akwai 'yan takarar majalisar dokokin jiha 10,321 dake neman kujeru 993 na majalisun dokokin jihohi a fadin kasar nan.

Ga dai cikakken jerin da INEC ta fitar a nan.

Gwamnonin dake neman tazarce

Babajide Sanwo-Olu

Gwamnan jihar Legas zai nemi tazarce zuwa wa'adi na biyu a zaben 2023.

Sabanin wanda ya gada a zaben da ya gabata na 2019, Akinwunmi Ambode, wanda ya rasa tikitin komawa takara, Sanwo Olu ya samu karbuwa a idon shugabannin APC.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asirin wasu gwamnoni, ya ce suna ba tsageru bindigogi AK-47 a lokacin zabe

Sanwo-Olu na da damar iya lashe zabe mai zuwa domin kammala wa'adi na biyu kasancewar jam'iyyar adawa bata da wani tasiri a bangarensa.

Seyi Makinde

Gwamna Seyi Makinde na Oyo na neman zarcewa zuwa wa'adi na biyu na mulki idan dama ta samu a 2023.

Idan Makinde ya lashe zaben, zai zama gwamna na biyu da ya taba yin wa'adin mulki sau biyu a tahirin Oyo.

Sai dai, yiwuwar ya lashe zaben na da wuya, domin kuwa damarsa 50% ce a zaben na 2023 mai zuwa domin kuwa yadda ya zo a zaben 2019 ya rushe a yanzu.

Ahmadu Finiti

Gwamnan PDP a jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri babban na gaban goshin dan takarar shugaban kasan jam'iyyar adawa ta PDP ne, Atiku Abubakar.

Akwai hasken Fintiri ya iya lashe zaben 2023 duba da dandazon jama'ar dake shiga PDP a 'yan kwanakin nan a jihar.

A baya kadan, gwamnan ya yiwa 'yan jam'iyyu daban-daban wanka a jiharsa yayin da suka tuba zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: BoT na PDP ta kammala zama da gwamnan da ke ba Atiku ciwon kai

Babagana Zulum

Gwamnan APC Zulum na daya daga cikin gwamnonin da jama'a ke kauna, musamman 'yan jiharsa.

Gwamnatinsa ta sha fama da rashin tsaro, musamman ganin cewa jiharsa ce tushen kungiyar ta'addanci ta Boko Haram/ISWAP.

Babu shakka Zulum na da damar lashe zaben 2023, kamar dai a ce 80% cikin dari.

Inuwa Yahaya

Gwamna Yahaya na Gombe ya lashe zaben fidda gwani da kuri'u 563 a kwanakin baya.

Wani mai sharhi ya bayyana cewa, gwamnatin Inuwa Yahaya ta cika da yawan alkawuran da ta dauka, kuma tabbas ya kawo sauyi da dama a jihar ta Gombe.

Wannan na nuna cewa, akwai yiwuwar Inuwa Yahaya ya sake lashe zaben gwamna a 2023.

Bala Mohammed

Gwamnan Bauchi na yanzu na daga cikin gwamnonin dake neman tazarce a zaben 2023 mai zuwa nan kusa.

A baya-bayan nan, gwamnan ya karbi sabbin shiga PDP masu yawan gaske a jiharsa.

Gwamnan ya tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar su ta PDP kafin daga bisani ya rasa tikiti, aka sake zaben fidda gwanin gwamna a jihar kuma ya lashe.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

Sauran gwamnonin sun hada da:

AbdulRahman AbdulRazaq - APC-Kwara

Abdullahi Sule - APC-Nasarawa

Dapo Abiodun - APC-Ogun

Bello Matawalle - APC-Zamfara

Atiku, Ayu, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Taru a Bauchi, Za Su Tattauna

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gana da gwamnonin PDP a Arewa maso Gabas da sauran jiga-jigan siyasar yankin.

Wannan ganawa na zuwa daidai lokacin da Atiku ke ci gaba da samun ciwon kai daga gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kan wasu bukatun da ya gabatar ciki har da na sauke shugaban PDP na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.