Na Hannun Daman Dankwanbo da Wasu Jiga-Jigan PDP 4 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Gombe

Na Hannun Daman Dankwanbo da Wasu Jiga-Jigan PDP 4 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Gombe

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tayi babban kamu a jihar Gombe gabannin babban zaben 2023

  • Na hannun daman Ibrahim Hassan Dankwambo, Alhaji Ahmed Abubakar Walama da wasu jiga-jigan PDP hudu sun sauya sheka zuwa APC
  • Dankwambo yana neman takarar sanata kuma yana tare da tsagin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar

Gombe - Alhaji Ahmed Abubakar Walama, na hannun daman tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya sauya sheka daga Peoples Democratic Party (PDP), zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Walama ya rike mukamin kwamishinan karamar hukuma da harkokin sarauna karkashin gwamnatin Dankwambo daga 2011 zuwa 2019.

Ibrahim Dankwanbo
Na Hannun Daman Dankwanbo da Wasu Jiga-Jigan PDP 4 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Gombe Hoto: Business Post Nigeria
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika wani kwamishina a mulkin Dankwambo na biyu, Sa’idu Kawuwa Malala, shima ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023

Daily Trust ta kuma rahoto cewa wani tsohon mai ba jihar shawara na musamman, Maigari Usman Malala, tsohon sakataren PDP a yankin Gombe ta arewa, Mohammed Ya’u da mataimakin ma’ajin jihar, Baba Bawa, sun bar jam’iyyar adawar zuwa APC.

Sabbin mambobin na APC sun karbi katin rijistansu da ke nuna su din ‘ya’yan jam’iyyar mai mulki ne a yanzu rahoton Nigerian Tribune.

Dankwambo, wanda ya kasance babban jagoran PDP a jihar yana takarar kujerar sanata mai wakiltan Gombe ta arewa karkashin PDP.

Tsohon gwamnan zai fafata da sanata mai ci, Sa’idu Ahmed Alkali na APC, wanda ya kayar dashi a 2019.

Yayin da babbar jam’iyyar adawar kasar ke cikin rikici tsamo-tsamo, Dankwambo na a tsagin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Bai hallara a taron karshen mako ba, lokacin da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya ziyarci jihar don bude ofishin kamfen din da jigon jam’iyyar, Jamilu Isyaku Gwamna ya bayar da gudunmawa.

Kara karanta wannan

Fushin Gwamnoni: Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Ganawar Gwamna Wike da Wasu Gwamnonin Tsaginsa Ya Kara Hargitsa Jam'iyyar PDP

A wani labarin, mun ji cewa shirun da gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) biyar masu biyayya ga tsagin Nyesome Wike na jihar Ribas suka yi ya sa cikin shugabannin jam’iyyar ya duri ruwa.

A ranar Lahadi ne gwamnonin da suka hada da Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Wike suka gana a Enugu.

An rahoto cewa sun saka labulen ne domin daukar matsaya kan rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawar kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel