Dan Majalisar Tarayya Ya Yi Kira Da A Rushe Majalisar Dattawan Najeriya Domin A Rage Kashe Kudade

Dan Majalisar Tarayya Ya Yi Kira Da A Rushe Majalisar Dattawan Najeriya Domin A Rage Kashe Kudade

  • Jigon siyasa a Najeriya ya ce, ci gaban kowace kasa ya ta'allaka ne da ingancin gwamnati da 'yan siyasar kasar ke bayarwa
  • A Najeriya, lamarin ya sha bamban, domin kuwa da yawan wasu 'yan siyasa na ganin rike madafun iko a matsayin damar da za su rarumi kudade
  • Abin ban sha'awa, mamba a majalisa ne ya dago wani batu mai ban mamaki, inda yace ya kamata a rushe majalisar dattawan kasar

FCT, Abuja - Wani rahoton jaridar Daily Sun ya ce, mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Ovia a jihar Edo, Hon Denis Idahosa ya tada wani batu mai ban mamaki a ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba.

Denis ya yi kira da a soke majalisar dattawan kasar nan tare da kirkirar majalisa ta bai daya domin rage kashe kudaden tafiyar da gwamnati a Najeriya.

Kara karanta wannan

Karramawar kasa: An samu tsaiko, gwamnati ta ce bata fitar da sunaye ba

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillacin labaran Najeriya ya yi dashi a Abuja.

Dan majalisa ya yi kira a rushe majalisar dattawa saboda wasu dalilai
Dan Majalisar Tarayya Ya Yi Kira Da A Rushe Majalisar Dattawan Najeriya Domin A Rage Kashe Kudi | Hoto: dennisidahosa.com
Asali: UGC

A cewarsa, majalisar dattawa, wacce daya ce daga majalisun dokoki biyu da Najeriya ke dashi, kamata ya yi ta hakura matukar kasar ta bukaci zaftare kudaden da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati, rahoton Premium Times.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilan da dan majalisar ya bayar

A cewarsa:

"Na yi imani da cewa, kamata ya yi a rushe majalisar dattawa, ba wai saboda ni dan majalisar wakilai bane, sai don da yawa daga ayyukan majalisa ana yinsu ne a majalisar kasa, wacce itace majalisar wakilai.
"Kuma don a rage yawan kashe kudade. Muna da karancin kayan aiki a matsayinmu na kasa. Don haka ina ganin ace muna da majalisu guda biyu ba dabara bace.
"Idan muna son rage kudaden da ake kashewa, inaga kamata ya yi a rushe daya daga zaurukan, wanda a ra'ayina majalisar dattawa ya kamata a rushe.

Kara karanta wannan

Najeriya a hannun APC kamar mota ce a hannun direbanta ya sha giya ya bugu, inji jigon PDP

"Dalili kuwa shine, muna zama ne sau uku a mako. Ana biyanmu ne mu yiwa 'yan Najeriya aiki; za mu iya kara zaman zuwa kwanaki biyar a mako, yayin da za mu mallaki zaure daya da zai kula da komai.
"Saboda haka ina tunanin domin rage kashe kudi ba gaira ba dalili da yanzu muke gani, mafi kyau shine a rage zuwa zaure daya don samun daidaito."

Ba Mu Fitar da Jerin Sunayen Wadanda Za a Ba Lambar Karramawar Kasa Ba, Inji Gwamnatin Buhari

A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, jerangiyar sunayen da ke yawo a gidajen labaran yanar gizo a kwanakin nan na wadanda gwamnati za ta karrama na bogi ne, Daily Trust.

An yada wani jerin sunaye mai dauke da sunan marigayi shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Abba Kyari da wasu mutum 436 ya karade kafafen sada zumunta da kafafen yada labarai.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Kasar Uganda Ya Sace Zukata Bayan Ya Yi Hudubar Juma’a Cikin Harshen Larabci, Yana Aiki Ne A Qatar

A cikin jerin, akwai kuma su mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, magatakardar hukumar jarrabawar JAMB, Ishaq Oloyede da daraktar WTO Ngozi Okonjo Iweala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel