Yadda Dan Kasar Uganda Ya Sace Zukata Bayan Ya Yi Hudubar Juma’a Cikin Harshen Larabci, Yana Aiki Ne A Qatar

Yadda Dan Kasar Uganda Ya Sace Zukata Bayan Ya Yi Hudubar Juma’a Cikin Harshen Larabci, Yana Aiki Ne A Qatar

  • Wani mutumin kasar Uganda da ke aiki a gidan mai a Qatar ya sace zukata da dama bayan ya gabatar da hudubar Juma'a a harshen Larabci
  • Mutumin wanda ke sanye da kayan aiki ya wakilci limamin masallacin wanda yayi lattin zuwa sauke hakkinsa na addini a birnin Doha
  • Matashin ya yiwa dandazon jama'ar da suka taru nasiha ba tare da ya duba kowani littafi ba

An karrama tare da jinjinawa wani mutumin kasar Uganda da ke aiki a wani gidan mai a Qatar bayan ya wakilci wani limami wajen bayar da huduba a masallacin Juma'a.

Dan Uganda
Yadda Dan Kasar Uganda Ya Sace Zukata Bayan Ya Yi Hudubar Juma’a Cikin Harshen Larabaci, Yana Aiki Ne A Qatar Hoto: Ajyal Educational Centre.
Asali: UGC

Jarumin maza Abdul Rahman

Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuno Abdul Rahman Abdul Rashid kan mumbarin masallaci sanye da kayan aiki yayin da yake huduba cikin harshen Larabci sai kace balaraben usuli.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: Gwamnati ta yi laushi, ta fara lallabi da rokon ASUU ta janye yaji

Cibiyar ilimi na kasar Qatar da ke kula da harkokin matasa wato Ajyal ta karrama mutumin kasar Ugandan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon wanda aka yada a shafin Cibiyar ilimi na Ajial na twitter ya nuno Matashin yana huduba ba tare da ya duba kowani littafi ba, an kuma jinjina masa kan haddace ayoyi daga Al-qur'ani mai girma.

Ajial ta wallafa a twitter:

"A kokarin tallata kyawawan dabi'u da koyarwar addinin Musulunci, mutanen da ke cikin wannan shiri sun karrama dan Uganda da ke aiki a kamfanin gas."

Cibiyar ta masa maraba da zuwa a wani kasaitaccen liyafa inda yara suka dungi jefa masa furanni cike da farin ciki.

An karrama dan Ugandan

An rahoto cewa Matashin dan Ugandan ya hallara don jagorantar masallata a wani dan karamin masallaci da ke kusa da filin jirgin sama na Hamad.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa ya fadi abu daya zai yi ya magance yajin ASUU

A Bidiyon karrama dan Ugandan, cibiyar ta bayyana cewa shirin"Wathiq" na wannan shekarar zai karkata ne wajen magance lamarin cin zarafi.

Ta kuma lissafa darajar dan Adam a zahiri kuma cewa hakan baya kyautata kamanninsa.

Ka Fi Mai Hannu: Matashin Da Bai Da Hannaye Ya Ba Da Mamaki Yayin da Yake Tuka Mota Kamar Kwararren Direba

A wani labarin, wani mutumin kasar Kenya mai suna Sammy Bravo ya burge mutane da dama a soshiyal midiya saboda tarin baiwar da Allah yayi masa.

Abun da yasa labarinsa ya bayar da mamaki shine ganin cewa an haife shi ba tare da hannaye ba, amma kuma yana iya yin abubuwa da dama da masu hannu ke yi.

An gano Sammy, wanda ke karfafawa mutane gwiwa da zantuka yana ayyuka ba tare da taimakon wani ba ciki harda tuka mota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng