Ba Mu Fitar da Jerin Sunayen Wadanda Za a Ba Lambar Karramawar Kasa Ba, Inji Gwamnatin Buhari

Ba Mu Fitar da Jerin Sunayen Wadanda Za a Ba Lambar Karramawar Kasa Ba, Inji Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana bacin ranta ga yadda wasu bata-gari ke yada labaran karya kan abubuwan da ke tafiya a harkokin gwamnati
  • An yada wani jerin sunaye da ke nuna wadanda gwamnatin Najeriya za ta ba lambobin yabo da karramawa bisa jajircewarsu a Najeriya
  • Gwamnati ta ce tabbas za a ba da lambobin yabo na karramawar kasa, amma ba a fidda sunayen wadanda za su samu karramawar ba

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, jerangiyar sunayen da ke yawo a gidajen labaran yanar gizo a kwanakin nan na wadanda gwamnati za ta karrama na bogi ne, Daily Trust.

An yada wani jerin sunaye mai dauke da sunan marigayi shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Abba Kyari da wasu mutum 436 ya karade kafafen sada zumunta da kafafen yada labarai.

Kara karanta wannan

Allah na tuba: Malamin addini ya karbi kudin Tinubu, ya yi nadamar abin da ya aikata

A cikin jerin, akwai kuma su mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, magatakardar hukumar jarrabawar JAMB, Ishaq Oloyede da daraktar WTO Ngozi Okonjo Iweala.

Gwamnati ta magantu kan batun karramawar kasa
FG: Ba Mu Fitar da Jerin Sunayen Wadanda Za a Ba Lambar Karramawar Kasa Ba | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An kuma ruwaito cewa, za a yi wannan bikin karramawan ne a ranar 11 ga Oktoba a fadar shugaban kasa da ke Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba gaskiya bane, ba a fitar da jerin sunayen ba, inji gwamnatin Buhari

Sai dai, a wata sanarwa da ta fitar ta hannin daraktan yada labarai na ma'aikatar ayyuka na musamman, Julie Jacobs, gwamnati ta ce tabbas Buhari zai karrama 'yan Najeriya da abokai na kasar, amma ba a cire sahihin jerin sunayen ba.

Gwamnatin Buhari ta kuma nuna fushi da damuwa ga yadda wasu bata-gari ke yada labaran karya don cimma wata manufa, rahoton Punch.

Rabaran Mbaka Ya Magantu Kan Zaben 2023, Ya Ce Wasu ’Yan Najeriya Na Bata Lokacinsu Ne Kawai

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa ya fadi abu daya zai yi ya magance yajin ASUU

A wani labarin, Rabaran Eike Mbaka na Adoration Ministry da ke Emene a jihar Enugu ya magantu kan zaben 2023 da ke karatowa a nan gaba kadan, rahoton Tribune Online.

Ya yi magana mai daukar hankali a jiya Lahadi 2 ga watan Oktoba, inda ya bayyana abubuwan da ya hango kan zaben mai zuwa.

Wannan karon ne dai karon farko da Mbaka ya yi magana tun bayan dage takunkumin hana shi wa'azi da kungiyar kiristoci ta yi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel