Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

  • 'Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar LP, Pter Obi, ya sanar da cewa zai inganta rayuwar talakan Najeriya idan ya ci zabe
  • Ya tabbatar da cewa, zai bai wa matasa fifiko tare da tabbatar da inshorar lafiya ga talakawan Najeriya 100 miliyan
  • A fannin ilimi kuwa, Obi yace zai inganta shi tare da tabbatar da an samu jarin sana''i kananan da matsakaita

Ebonyi - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP), ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga rayuwar talakawan Najeriya idan aka zabe shi.

Da yake jawabi a wani taro a ranar Asabar a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, Obi ya ce za a saka al'ummar Najeriya cikin tsare manufofi da gudanar da mulki, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

Peter Obi
Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce matasan Najeriya ne za su kasance masu kurba daga ajandar sa ta sauya tattalin arzikin kasar.

“Babban aikin shugabancinmu a 2023 shi ne daidaita harkokin mulki da kuma tabbatar da abinda ya dace, da kawo sauyi, da kuma tasiri. Za mu nuna cewa shugabanci nagari ya shafi samar da ayyukan da ake bukata ga jama’a."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Obi yace.

“Idan aka zabe ni a matsayin shugaban Najeriya na gaba, matasa za su kasance manyan mora daga babbar ajandar da zan yi na sauya Najeriya daga kasa mai ci zuwa kasa mai albarka. Manyan bangarorin biyu na wannan ajanda dai su ne bunkasa jarin dan Adam da harkokin kudi.
"A karkashin jagorancina, gwamnatin tarayya za ta ba da fifikon a tsarin ilimi don samar da kwararrun ma'aikata da suka dace da bukatar kasuwar kwadago ta karni na 21, tare da samar da ilimin kasuwanci a dukkan matakai."

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

- Yace.

Obi ya ce kiwon lafiya da ilimi na da matukar muhimmanci ga ci gaban Najeriya, inda ya yi alkawarin tabbatar da “a ƙalla talakawan Najeriya miliyan 100 sun samu kulawar lafiya kyauta”.

A cewar bankin duniya, adadin talakawan Najeriya zai kai miliyan 95.1 a shekarar 2022.

“Saboda rawar da kiwon lafiya ke takawa wajen karfafa ilimi a ma’auni na samar da aiki, shugabanci na zai mayar da hankali sosai kan tsarin kiwon lafiya ta hanyar tabbatar da cewa a kalla talakawan Najeriya miliyan 100 sun sami damar yin ayyukan kiwon lafiya kyauta ta hanyar hadaddiyar tsarin inshorar lafiya.
“Idan aka zabe mu, mun kudiri aniyar samar da Asusun Samar da Ma’auni na SME da ke tafiyar da sana’a a cikin shekarar farko ta zamana a ofis da nufin bunkasa ci gaban a kalla masana’antu masu kara darajar da za su yi amfani da albarkatun kasa, walau na noma ko na ma’adinai. a kowace karamar hukuma a Najeriya.”

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

A wani labari na daban, Gwamna Nyesom Wike, a ranar Juma'a, ya sanar da cewa shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, yana neman mukamin sakataren gwamnatin tarayya idan jam'iyyar ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

A cewarsa, hakan na iya taimaka masa wurin rike mukaminsa na shugaban jam'iyya na kasa da kuma dagewarsa na kada ya sauka daga mukaminsa domin tabbatar da gaskiya da adalci, Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel