Shinkafa da Wake: Abin da Ya Sa Mu Ke Tare da Tinubu ba Kwankwaso ba inji ‘Yan NNPP

Shinkafa da Wake: Abin da Ya Sa Mu Ke Tare da Tinubu ba Kwankwaso ba inji ‘Yan NNPP

  • Fustatattun ‘Ya ‘yan jam’iyyar NNPP na jihar Osun sun bada uzurinsu na bin tafiyar Asiwaju Bola Tinubu
  • Clement Bamigbola ya yi wa shugaban NNPP na Osun raddi, yace sam Abdusalam Abiola bai san kan siyasa ba
  • ‘Dan siyasar yace jam’iyyar hamayyar ta mutu a reshen jihar, shiyasa suka tattara kayansu zuwa APC mai mulki

Osun - Mutum hudu da suka nemi takarar majalisar tarayya a jihar Osun a karkashin inuwar NNPP, sun bayyana dalilinsu na marawa Bola Tinubu baya.

Punch ta rahoto wadannan ‘yan siyasa suna cewa sun lura jam’iyyarsu ta NNPP za ta ruguje a jihar Osun, wannan ne ya sa suka koma goyon bayan APC.

Shugaban ‘yan wannan tafiya, Clement Bamigbola ya fitar da jawabi a matsayin martani ga shugaban NNPP na rikon kwarya, Abdusalam Abiola.

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Bola Tinubu da Uba Sani Sun Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Mambobin PDP a Kaduna

A baya, Abdusalam Abiola ya fito yana cewa jam’iyyar NNPP ta reshen jihar Osun ba za tayi rashi saboda wadannan ‘yan siyasa sun fice daga cikinta ba.

Ba ku iya siyasa ba - Clement Bamigbola ga NNPP

Amma da yake maida martani a madadin sauran mutanensa, Clement Bamigbola ya yi hasashen cewa NNPP mai kayan dadi ba za ta kai labari a 2023 ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan siyasar yace a halin yanzu, jam’iyyar NNPP ta mutu murus idan ana maganar jihar Osun.

Kwankwaso
Sanata Kwankwaso zai bude ofishin NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Bamigbola wanda ya nemi tikitin takarar Sanatan yace shugaban NNPP na reshen jiharsu bai fahimci siyasa ba tun da zai ce wasu ba su da amfani ba.

Abin da ya kai mu wajen Tinubu

“Dalilinmu na goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu a zaben shugaban kasa shi ne hango wargajewar da ke jiran jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Wasu 'Ya'Yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC Ana Tsaka da Rikici

Abin takaici ne shugaban rikon kwarya na jam’iyya zai rika cewa ‘yan takara ba su da amfani.
Wannan ya nuna bai san komai a kan harkar siyasa ba. Yanzu haka maganar da ake yi, jam’iyyar NNPP ta mutu a jihar Osun.”

- Clement Bamigbola

Su wanene suka juya baya?

Sauran fusatattun ‘ya ‘yan NNPP da suka tsallaka wajen Tinubu bayan sun gagara samun tikiti sun hada da Bolaji Akinyode wanda ke harin Sanata.

Ragowar su ne Oluwaseyi Ajayi da Olalekan Fabayo wanda suka nemi jam’iyyar ta tsaida su a matsayin ‘yan takarar majalisar wakilan tarayya a 2023.

Za mu yi nasara - Sakataren NNPP

A game da zaben shugaban kasa, Legit.ng Hausa tayi magana da Aliyu Adamu Kwankwaso wanda shi ne Sakataren NNPP na reshen jihar Enugu.

'Dan siyasar ya shaida mana cewa 'dan takarasu watau Rabiu Kwankwaso zai yi nasara domin NNPP ta tsaida 'yan takara a kowane kujera a Kudu.

Kara karanta wannan

Wike Ya Jawo Atiku Abubakar Ya yi wa Bola Tinubu Raddi Yayin da Ake Yaki a PDP

PDP, APC sun gaza - Kwankwaso

Kwanakin baya an ji labari Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki PDP da APC, ya ce gwamnatocin da aka yi a baya sun gaza biyawa jama'a bukatunsu.

‘Dan takaran shugaban kasar ya tallata jam’iyyarsa ta NNPP wanda aka sani da mai kayan dadi da ya kai ziyara zuwa jihar Ekiti a kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel