Wike Ya Jawo Atiku Abubakar Ya yi wa Bola Tinubu Raddi Yayin da Ake Yaki a PDP

Wike Ya Jawo Atiku Abubakar Ya yi wa Bola Tinubu Raddi Yayin da Ake Yaki a PDP

  • Kwamitin yakin takarar Atiku Abubakar a zaben 2003 ya fitar da raddi na musamman ga Bola Ahmed Tinubu
  • Paul Ibe da ya yi magana, ya yi martani ne a game da sukar Atiku da Tinubu yayi saboda wasu kalaman Nyesom Wike
  • Ibe yace ‘dan takaran na jam’iyyar APC ya shirya bayanin inda ya yi karatu, a maimakon yi wa PDP katsalandan

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP, ya yi raddi Bola Ahmed Tinubu mai neman shugabancin kasa a APC mai mulki.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Juma’a cewa mutanen Atiku Abubakar sun nemi Bola Tinubu ya kare kan shi daga sukar da al’umma suke yi masa a yau.

Wasu sun kalubalanci ‘dan takaran shugaban kasar na APC da ya fito da takardun shaidar karatunsa, domin ya gamsarwa Duniya cewa ya je makaranta.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Fallasa Sirrin Zaman da Ya yi da su Bola Tinubu a Kasar Waje

Hadimin ‘dan takaran PDP na 2023, Paul Ibe ya fadawa Tinubu ya yi wa ‘Yan Najeriya bayanin inda ya yi karatunsa, kafin ya fara fitowa yana maganar PDP.

Tinubu: Karyarka ta kare yanzu - Atiku

Daily Post ta rahoto Mista Ibe yana cewa rigimar cikin gidan jam’iyyar APC ya tona asirin Tinubu wanda duk abin da ake yi, ba a ji duriyarsa ba sai yanzu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A maimakon ya maida hankali wajen tallata kansa a zabe, Ibe yace tsohon gwamnan na jihar Legas ya fi damuwa da sabanin da ake yi a jam’iyyar hamayya.

Atiku
Atiku Abubakar wajen taron PDP Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Tambayoyin mutane na jiran Tinubu

“Tun da kwamitin yakin neman zaben APC na shugaban kasa sun farka daga gyangyadinsu, zai yi kyau a tuna masu akwai tambayoyin da ake jiran ‘dan takaransu ya amsa.”
Za mu yi mutunci wajen tunawa jam’iyyar APC cewa idan aka fara yakin neman zabe, nan ba da dadewa ba, ‘Yan Najeriya za su nemi jin amsar manyan zargin da ke kan ‘dan takararsu.

Kara karanta wannan

Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014

A maimakon bata lokacinsa a kan abin da bai shafe su ba, suyi amfani da lokacinsu inda ya dace.

Kamar yadda gidan rediyon Najeriya suka kawo rahoto dazu, Ibe yace maganar sabani tsakanin shugabannin PDP ba bakon lamari bane a tsarin siyasa.

APC za ta sha kasa a zaben 2023

Jawabin ya caccaki gwamnatin APC da Tinubu yake takara a karkashinta, kwamitin takarar tace gwamnatin nan ba ta tabuka abin kirki a shekara bakwai ba.

A karshe, Ibe ya yi wa APC barazanar cewa ta shirya shan kasa a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Hakan na zuwa ne bayan an ji Gwamna Nyesom Wike ya yabawa Bola Ahmed Tinubu, hakan ta sa ‘dan takaran ya samu damar caccakar Atiku Abaubakar.

Tinubu sun san daraja ta - Wike

An ji labari Nyesom Wike yace a zamansa da Asiwaju Bola Tinubu kwanaki, an yi masa tayin tikitin Sanata a zaben 2023 saboda irin adalcin ‘Dan takaran APC.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani Babban Na Hannun Daman Atiku Abubakar Ya Rasu

Daga baya ne aka ji Tinubu ya fake da rigimar cikin gidan jam'iyyar adawar, yake cewa Wazirin Adamawa ya gagara dinke PDP, sai ma ya buge da wargaza ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel