‘Dan takaran 2023, Kwankwaso ya yi maganar kyale NNPP domin ya hada-kai da Atiku

‘Dan takaran 2023, Kwankwaso ya yi maganar kyale NNPP domin ya hada-kai da Atiku

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki PDP da APC, ya ce gwamnatocin da aka yi a baya sun gaza
  • ‘Dan takaran shugaban kasar ya tallata jam’iyya mai kayan dadi da ya kai ziyara zuwa jihar Ekiti
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna ba zai yi watsi da jam’iyyar NNPP, ya hada-kai da PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ekiti - Tsohon gwamnan Kano kuma ‘dan takara a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga mutane da su guji jam’iyyun APC da PDP.

Daily Trust ta rahoto Rabiu Musa Kwankwaso ya na mai kira ga mutanen Najeriya da su yi watsi da APC da takawararta PDP a zabe mai zuwa.

Da yake jawabi a garin Ado Ekiti, jihar Ekiti, ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa wadannan jam’iyyu biyu sun ba al’umma kunya.

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu Kwankwaso ya zama Mataimakin Peter Obi idan an hade ba inji Jibrin

A cewar Sanata Rabiu Kwankwaso, gwamnatocin APC da PDP ba su iya shawo kan matsalolin kasar nan, su kawo cigaban da ake bukata ba.

Jaridar New Telegraph ta ce ‘dan siyasan ya yi kira da babbar murya ga jama’a da su yi imani da jam’iyyar NNPP wajen ganin an kawo sauyi.

Kwankwaso ya ce a ‘yan watannin nan, jam’iyyar ta NNPP da suka farfado ta na ta samun kasuwa a bangarori da-dama a fadin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan takaran NNPP
Rabiu Musa Kwankwaso da Ayo Fayose a Ribas Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Jawabin Rabiu Kwankwaso

“Mun ga salon mulkin APC da na PDP, kuma dukkaninmu mun yarda cewa sun gaza, sun bada kunya kwarai da gaske.”
“Ka da a sa ran za su tabuka wani abin nan gaba. Mutanen da ke cikin wadannan jam’iyyu biyu ba su da abin da za su iya.”
“Duba titin Akure zuwa garin Ado-Ekiti, ya yi raga-raga sosai. Ku duba wasu daga cikin Biranen nan, ba za a ga komai ba.”

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta na marmarin Kwankwaso ya dawo, ta ce zai iya rike Najeriya nan gaba

“Talauci ya kai halin intaha a kasar nan. Sha’anin rashin tsaro ya kai karshe, ba za mu cigaba da zama a tashin hankali ba.”
“Yadda za a magance wannan shi ne a tallata manufofin NNPP, jam’iyya mai son cigaba, sannan a zabi jam’iyyar a 2023.”

Kwankwaso zai ba PDP goyon baya?

A karshen jawabinsa, jaridar ta ce Kwankwaso ya musanya rade-radin hada-kai da jam’iyyar PDP.

“Ka da a manta cewa NNPP ta na da ‘yan takara a ko ina a zaben 2023. Ana tunanin zan bar su, in shiga PDP? Ba za ta yiwu ba.

An ji labari Farouk Adamu Aliyu ya ce burinsu yadda za a lashe zaben 2023 mai zuwa, ba maganar addinin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa ba.

Hon. Farouk Adamu Aliyu ya ce ‘dan takarar mataimakin shugaban kasarsu zai iya zama Musulmi ko Kirista, ya ce muhimmin abu shi ne a lashe zabe.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike ya fadi dalilin da ya sa 'Dan takaran NNPP, Kwankwaso ya ziyarce shi a gida

Asali: Legit.ng

Online view pixel