Akwai Masu Zangon Kasa a Gwamnan Shugaba Buhari, Yahaya Bello

Akwai Masu Zangon Kasa a Gwamnan Shugaba Buhari, Yahaya Bello

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yace akwai wasu mutane dake yi wa gwamnatin Buhari zagon ƙasa
  • Gwamnan wanda aka naɗa shugaban matasan kamfe na kasa, yace akwai alamun tambaya a wasu alƙaluman NBS
  • Bello ya yi wannan bayanin ne yayin da yake tsokaci kan shirin jam'iyyar APC na tunkarar babban zaɓen 2023

Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, kuma shugaban matasa na yakin neman zaɓen Tinubu, yace akwai wasu mutane da hukumomi da ke yi wa gwamnatin shugaba Buhari, zagon ƙasa.

Yahaya Bello ya yi wannan zancen ne ranar Laraba yayin hira da Arise TV game da inda aka kwana a shirin APC na fara yakin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2023.

Yahaya Bello da Buhari
Akwai Masu Zangon Kasa a Gwamnan Shugaba Buhari, Yahaya Bello Hoto: Yahaya Bello
Asali: Twitter

Da aka nemi ya yi tsokaci kan tulin bashi, yawan matasa marasa aikin yi da damuwar ficewar kwararrun ma'aikatan lafiya a mulkin Buhari kamar yadda NBS ta fitar, gwamnan yace akwai alamun tambaya a wannan ƙididdiga.

Kara karanta wannan

2023: Dole Mu Tabbatar da Najeriya Gabanin Shugaban Kasa, Jonathan

Gwamna Bello ya ƙara da cewa tun zuwan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bai yi wa hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) garambawul ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa da Daily Trust ta ruwaito, Yahaya Bello yace:

"Mafi yawan lokaci muna da shakku da tambaya a irin waɗannan kididdiga saboda ni abun ya fi shafa a mafi yawan lokuta. Alal misali NBS ko a kafafen labarai, mutane sun ce Kogi ta rike wa ma'aikata albashi ko ba'a biyan albashi."
"Ta kai ga wani mai tsoma baki ya sanya a Facebook cewa na rike wa ma'aikatan Kogi albashin watanni 12 ko 18. Kuma mutumin shugaba ne a ɓangarensa, amma cikin awanni ya gane dole ya goge rubutun."
"Saboda haka akwai wasu gurbatattun bayanai da ake yaɗa wa. Amma haka ba yana nufin wannan gwamnatin ba ta da laifi bane, sai dai maganar gaskiya akwai masu zagon kasa. Duk ɗa haka shugaban ƙasa na kokari."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Neja, Sun Halaka Rayukan Bayin Allah

Ba'a sake fasalin NBC yadda ya dace ba - Bello

Game da batun hukumar NBC, gwamna Bello yace shugaban kasa bai yi wa hukumar kwaskwarima yadda ya dace ba tun da ya gaje ta, the cable ta ruwaito.

"Ba zai yuwu su riƙa sakin lambobi yadda ransu ke so ba suna zagon ƙasa, idan suna so mu yarda da su, akwai bukatar su nuna mana dabaru da matakan da suka bi suka samo wannan adadin."

A wani labarin kuma Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Koma Bayan Tinubu a Zaɓen 2023

Jam'iyyar PDM, wacce marigayi Shehu Musa Yar'adua ya kafa daga baya ta koma tafiyar siyasar Atiku, ta yi watsi da tsohon mataimakin shugaban.

Jam'iyyar wacce aka rushe ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu na APC tare da wasu ƙungiyoyi, sun ce shi ya fi dacewa da shugabanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel