2023: Tinubu Ya Naɗa Gwamna Bello Matsayin Shugaban Yakin Neman Zabe Na Matasa

2023: Tinubu Ya Naɗa Gwamna Bello Matsayin Shugaban Yakin Neman Zabe Na Matasa

  • Bola Ahmed Tinubu, mai neman kujerar shugaban ƙasa a inuwar APC, ya naɗa Yahaya Bello shugaban matasan Kamfen ɗinsa
  • Gwamna Bello na jihar Kogi ya samu goyon bayan matasa da mata a sassan Najeriya gabanin zaɓen fidda gwanin APC
  • Bello Ya karɓi naɗin tare da shan alwashin yin duk me yuwuwa wajen ganin Tinubu/Shettima sun yi nasara a 2023

Abuja - An naɗa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin shugaban matasan tawagar yakin neman zaɓen Tinubu-Shettima a jam'iyyar APC.

Vanguard ta ruwaito cewa wannan naɗin na cikin wata takarda mai adireshin Yahaya Bello ɗauke da sa hannun ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Bola Tinubu da Yahaya Bello.
2023: Tinubu Ya Naɗa Gwamna Bello Matsayin Shugaban Yakin Neman Zabe Na Matasa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A takardar Tinubu ya jaddada cewa gwamna Bello na ɗaya daga cikin manema tikitin takara a zaɓen fidda gwanin APC ta suka cancanci wannan babban matsayi duba da nasarorinsa a matsayin gwamna da mamban jam'iyya.

Kara karanta wannan

2023: Babban Cikas, 'Yan Arewa a Jihohi Shida Sun Watsar da Atiku, Sun Faɗi Wanda Suke so Ya Gaji Buhari

Tsohon gwamnan Legas ya ƙara da cewa gwamnan na Kogi zai yi duk me yuwuwa wajen sauke nauyin da aka dora masa da isar da sakon Kamfe, wanda zai zama fitila ga nasara a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan baku manta ba gabanin zaɓen fidda gwanin APC, mata da matasa daga dukkan shiyyoyi shida na Najeriya sun ayyana goyon bayansu ga Yahaya Bello.

Daily Trust tace Wasikar wacce a kai wa taken, "Naɗin shugaban tawagar matasa na ƙungiyar Kamfen din Tinubu/Shettima ta ƙasa," wani sashin sakon cikinta yace:

"Ta wannan wasika, muna farin cikin naɗa ka shugaban tawagar matasa na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima ta ƙasa. Naɗin ya je inda ya dace kuma a kan lokaci duba da nasarori da ka samu a matsayin gwamna."
"Mun ji daɗin shigowarka cikin kungiyar Kamfe, mun san zaka yi duk me yuwuwa wajen sauke nauyin da aka ɗora maka da isar da saƙon kamfe, wanda zai kai mu ga ɗare wa kujera lamba ɗaya a 2023."

Kara karanta wannan

2023: Matsala ga Atiku, Jigon PDP da Wasu Shugabanni Sun Yi Murabus, Sun Koma APC

Gwamna Bello Ya karɓi naɗin hannu biyu

A wasikar amincewa da naɗin, gwamna Bello ya alwashin baje basirarsa, aiki kafaɗa da kafaɗa da ɗan takarar shugaban ƙasa wajen tabbatar da nasarar APC.

"Ranka ya ɗaɗe kai mutum ne da na sani, wanda ba wai zama abin koyi ba kaɗai, har da kokarin samar da shugabanci mai nagarta da nake wa Najeriya fata na tsaro da haɗin kai."

A wani labarin kuma Tsagin Wike Sun Bazo Wuta, Atiku Ya Kafa Sharuɗdan Tunɓuke Shugaban PDP Na Ƙasa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace sauke Ayu abu ne mai sauki amma dole a bi matakan doka da ƙa'idojin kwansutushin.

Yayin ziyarar da ya kai Ibadan, jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde ya kara jaddada cewa dole shugaban PDP ya yi murabus kafin 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel