Peter Obi Ya Yi Magana Da CNN, Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Arewacin Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa
- Mr Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben shekarar 2023 ya yi hira da Asher Zain na gidan talabijin na CNN
- Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya shaida mata cewa idan aka zabe shi shugaban kasa abin da zai fara yi shine magance rashin tsaro a kasar
- Obi ya kuma bayyana cewa zai mayar da hankali wurin ganin ya farfado da ayyukan noma a arewacin Najeriya domin hakan zai taimakawa tattalin arziki
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wurin magance matsalar tsaro don farfado da noma a arewa.
A hirar da ya yi da Asher Zain a tashar Cable News Network International, CNN, a ranar Juma'a, Obi ya ce idan aka zabe shi a 2023, abin da zai mayar da hankali a farkon kwanakinsa a ofis sune dawo da zaman lafiya a arewa saboda rashin tsaro na nakasa tattalin arziki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Zain ta masa tambaya kan shirin da ya ke da shi na farfado da tattalin arzikin Najeriya, ya ce:
"Na farko, shine dole ka magance batun rashin tsaro saboda yana kawo cikas ga tattalin arzikin kasar.
"Ya kamata ka tabbatar manoma sun koma gona kuma ka tabbatar cewa an saka hannun jari a kasar noma da ke arewa ana noma; ya kamata ka fara tsamo mutane daga talauci cikin gaggawa.
"Ya kamata ka rage kudaden da ake kashewa wurin tafiyar da gwamnati da batun rashawa."
Ya ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ya cancanta, kuma wanda ke da basira da hangen nesa da zai iya magance kallubalen bashi, satar danyen mai, rashawa da tattalin arziki da ya tabarbare.
Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP
A wani rahoton, hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya ce dan takarar shuganan kasa na Labour Party, LP, Peter Obi ya rasa kuri'un yarbawa saboda yi wa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar APC izgili.
Omokri, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Satumba ta shafinsa na Twitter kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Asali: Legit.ng