Akwai Yiwuwar PDP Za Ta Sha Kaye A Zaben Shugaban Kasa Na 2023, In Ji Jigon PDP Mai Karfin Fada A Ji
- Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Bode George ya yi gargadin cewa jam'iyyar tana iya shan kaye a zaben 2023 saboda rikicin shugabanci
- Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa ya shawarci Iyorchia Ayu ya cika alkawarin da ya dauka ya yi murabus tunda dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa ya fito daga arewa
- George ya bada shawarar a nada dan kudu maso yamma shugabancin jam'iyyar PDP don yankin ta dena ganin kamar an ware ta idan ba haka ba ba dole bane su bada kuri'a a 2023
Jihar Legas - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Cif Bode George ya gargadi jam'iyyar hamayyar cewa za ta iya shan kaye a zaben 2023 saboda rikicinta, The Nation ta rahoto.
Ya ce yadda har yanzu aka gaza warware matsalar shugabanci a jam'iyyar zai iya shafan makomarsu a zaben 2023.
George, ya yi gargadin cewa PDP tana iya rabuwa biyu Jam'iyyar PDP ta Arewa da Jam'iyyar PDP ta Kudu, idan shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ki yin murabus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Bari in fadi karara cewa shugaban jam'iyya na kasa da dan takarar shugaban kasa ba za su iya fitowa daga yanki guda daya ba."
George, wanda tsohon sojan ruwa ne, ya yi magana ne da manema labarai kan tasirin siyasar bangarenci da rashin daidaita a jam'iyyar.
Ina bawa Ayu shawara ya yi murabus - George
Jigon jam'iyyar na PDP ya shawarci Ayu ya cika alkawarinsa na sauka, idan dan takarar shugaban kasa ya fito daga arewa.
Ya koka kan cewa PDP ta saba ka'idar tafiyar tare da kowa, domin dan takarar shugaban kasa da ciyaman na kasa duk yan arewa ne.
A bawa kudu maso yamma shugabancin jam'iyyar PDP - George
George ya ce zai dace a bawa yankin kudu maso yamma mukamin shugaban jam'iyya na kasa don kada su rika jin kamar an ware su kuma ba a musu adalci ba.
Jagoran jam'iyyar ya ce PDP na fuskantar 'babban hatsari' da zai iya kawo mata cikas wurin samun nasara a zabe.
Wani sashi cikin kalamansa:
"Kada mu bari wani san rai - na kabila ko addini ya raba mu. Idan aka yi la'akari da abin da ke faruwa yanzu, jam'iyyar mu na iya shan kaye a zaben shugaban kasa idan muka gaza warware matsalar zargin wariya da yan kudu ke ganin ana musu. Idan ba a magance matsalar ba, kada mu yi tsammanin samun kuri'a daga wurin su."
George ya ce dole jam'iyyar ta koma tsarin hadin kai, adalci, daidaito wadanda aka kafa ta idan ba haka ba za su sha kaye a zaben 2023.
Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015
A bangare guda, gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.
Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.
Asali: Legit.ng