Akwai Aiki A gaba: Sanatan PDP Ya Bayyana Abun Da Zai Faru Idan Ayu Ya Yi Murabus

Akwai Aiki A gaba: Sanatan PDP Ya Bayyana Abun Da Zai Faru Idan Ayu Ya Yi Murabus

  • Sanata Emmanuel Orker-Jev mai wakiltan Benue ta arewa maso yamma ya magantu a kan babban kalubalen da ke gaban jam'iyyar PDP
  • Orker-Jev ya ce babbar jam'iyyar adawar kasar za ta fada gagarumin rikici idan har shugabanta, Iyorchia Ayu ya yi murabus daga matsayinsa
  • Sanatan na PDP ya ce abun da ya fi dacewa a yanzu shine a kira babban taron jam'iyya don yin sulhu

Abuja - Sanata mai wakiltan yankin Benue ta arewa maso yamma, Emmanuel Orker-Jev, ya ce jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na iya tsintar kanta a ‘manyan rikice-rikice’ idan har shugabanta na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Sanatan wanda ya kasance jigon PDP ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da ya bayyana a shirin gidan talbijin din Channels na Sunday Politics.

Kara karanta wannan

"Dole Ya Sauka" Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Majalisar Koli Ta PDP Kan Ayu

Shugaban PDP na kasa
Akwai Aiki A gaba: Sanatan PDP Ya Bayyana Abun Da Zai Faru Idan Ayu Ya Yi Murabus Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Ayu na ta fuskantar matsin lamba a yan watannin da suka gaba, inda aka nemi yayi murabus daga bangarori daban-daban, musamman a sansanin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

A yayin da ake tsaka ga neman yayi murabus, kwamitin NEC na jam’iyyar ya nuna karfin gwiwa a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana kan ci gaban, Orker-Jev ya ce ya kamata a sulhunta batun kira ga Ayu yayi murabus.

Ya ce:

“Babban makiyin PDP zai zama PDP da kanta. A kullun, ina kwanciya da tashi da rashin nutsuwa da yadda abubuwa ke tafiya.”
“Ba wai cewa ba za a magance abubuwa bane, illa dai ba zai zama abu mai sauki bane. Murabus din shugaban kwamitin amintattu na daya daga cikin matakin neman maslaha ga matsalar.
“Ni lauya ne kuma na karanta kundin tsarin mulkin jam’iyyar. Idan Ayu ya janye a yau, me zai faru? Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a arewa shine dai zai karbi mulki idan aka bi kundin tsarin mulki. Idan mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa ya janye, toh zai tafi wajen mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: PDP ta fadi matsayar ta kan ko Ayu zai ci gaba da kasancewa shugabanta

“Ayu zai janye amma dole a sasanta ta yadda jam’iyyar ba za ta sake zurfafa a rikicin ba. Abu mafi kyau da zai iya faruwa shine cewa mu kira babban taro na musamman sannan mu ma sauya kundin tsarin jam’iyyar.”

Za Muyi Wa Atiku Ritaya, ‘Dan Ci-Ranin Siyasa Ne Daga Dubai Inji Kashim Shettima

A wani labarin, dan takarar jam'iyyar APC na kujerar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa Atiku Abubakar a zabe mai zuwa da za ayi.

The Nation ta rahoto Kashim Shettima yana mai cika baki a ranar Lahadi, 11 ga watan Satuma 2022, yace su za su yi nasara a zaben shugaban kasa.

Sanata Shettima yake cewa idan kwarewa a aiki, tarihi, iya jagoranci da gina shugabanni ake magana, Atiku ba zai iya karawa da Bola Tinubu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel