Tinubu, Atiku ko Obi? Bishop Kukah Ya Yi Magana Kan Irin Shugaban Da Najeriya Ya Dace Ta Zaba A 2023
- Babban malamin addini na Najeriya, Bishop Mathew Kukah, ya shawarci yan Najeriya kan abin da za su iya la'akari da shi wurin zaben shugaban kasa na gaba
- Archibishop na Sokoto ya ce ya kamata yan Najeriya su dena zabe saboda kabila, addini ko jam'iyya
- Bishop Kukah ya ce yan Najeriya su zabi mutumin da zai iya magance manyan kallubalen da kasar ke fuskanta
Bishop Mathew Kukah, Archibisjop na Sokoto, ya yi magana kan irin mutumin da ya kamata yan Najeriya su zaba don shugabancin kasar a 2023.
Malamin addinin da ake girmamawa ya ce yana da muhimmanci yan Najeriya su dena zabe saboda kabila, addini ko jam'iyya amma su zabi wanda zai iya magance manyan matsalolin da kasar ke fama da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kukah, a cewar The Punch, ya bada wannan shawarar ne yayin hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Juma'a 2 ga watan Satumba.
Bishop din ya ce duk da cewa yan takarar manya jam'iyyun da ake da su yanzu sun cancanci su jagoranci kasar, ya kamata yan Najeriya su musu duba na hakika su yi zabe da hikima.
Yan Najeriya su binciki akida da tsare-tsaren yan takarar shugaban kasa - Kukah
Kukah ya kara da cewa zamanin biya wa yan siyasa masu 'dadin baki' ya wuce kuma ya zama dole yan kasar su tantance su kuma yi wa tankarar tambaya kan akidunsu da tsare-tsare da tsarin gwamnatin da suke son kafa wa kafin su yanke shawarar wanda za su zaba.
Ya ce yana da muhimmanci yan siyasa, musamman yan takarar shugaban kasa su saurari matasa, su fahimci abin da ke damunsu, kuma su tsara ajandarsu ta yadda za su magance wa matasan abin da ke damunsu.
Kalamansa:
"Shaukin da ya debi mutane a zaben 2015 ya bace. Mutane sun fahimci cewa an musu karya kuma mun ga sakamakon amfani da addini wurin rudar mutane da aka yi.
"Matasan sun fahimci hakan yanzu kuma suna yin tambayoyin da suka dace. Ina karfafawa yan siyasa su tafi lunguna da sakuna su tallata wa yan Najeriya tsare-tsarensu.
"Mutane sun mayar da hankali sosai kan zaben da ke tafe kuma na yi murnan ganin yadda matasa suka mayar da hankali kan zaben kasar."
Bishop Kukah: Ban Yarda Da Tikitin Musulmi Da Musulmi Ba
A baya, Matthew Kukah, ya ce tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ta yi koma baya ne ga cigaban da ake samu na hada kan yan kasa, The Cable ta rahoto.
Kukah ya yi wannan jawabin ne a hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Alhamis.
Yanzu-Yanzu: Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Ɗaya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki
Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ya zabi Kashim Shettima, wanda shima musulmi ne a matsayin mataimakinsa.
Asali: Legit.ng