Jonathan: Najeriya Ta Kama Hanyar Koma Wa Mulkin Kama-Karya

Jonathan: Najeriya Ta Kama Hanyar Koma Wa Mulkin Kama-Karya

  • Dakta Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya ya yi gargadin cewa kasar ta kama hanyar mulkin kama karya
  • Jonathan ya zaburar da yan Najeriya su tashi su kare demokradiyyar da ake mora yanzu a kasar
  • Tsohon shugaban kasar ya kuma shawarci matasan kasar su tabbatar sun yi rajistan zabe su kuma fita su kada kuri'unsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya ce Najeriya ta kama hanyar gangarawa mulkin kama karya.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wurin taron bikin cika shekaru 70 na Bishop din cocin Katolika na Sokoto, Matthew Kukah, da aka yi a Sheraton Hotel a Abuja.

Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan: Najeriya Na Koma Wa Mulkin Kama-Karya. Hoto: @TheNationNews.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yanzun nan: EFCC ta kame kakakin majalisar wata jiha a filin jirgin sama

Da ya ke magana a wurin taron, Jonathan ya bukaci yan Najeriya su cigaba da sa ido su kuma zabi shugabanni da za su kai kasar tudun na tsira, rahoton Daily Trust.

Ya ce:

"Aikin da ke gaban mu shine kada mu yi sakaci, kada mu yarda demokradiyyar da muke mora ta bari basu mata barazana suyi nasara jefa kasar cikin mulkin kama karya, akwai alamun hakan a yanzu.
"Ka duba wasu jihohin, muna ganin wani abu da ke kama da gwamnatin kama karya amma demokradiyya ba ga cin zabe kawai ta tsaya ba, har da bawa kowa yanci.
"A matsayin mu na shugabanni a tsakiya da jihoji, musamman a wannan lokacin da zabe ke zuwa ya zama dole mu rika hakuri da mabanbantan ra'ayoyi."

Jonathan ya bukaci matasa su yi rajista su mallaki katin zabe su kuma tabbatar sun fita sun kada kuri'unsu a ranar zaben.

Sauran mayan mutane da suka halarci taron sun hada da Asiwaju Bola Tinubu, Kashim Shettima, Gwamna Kayode Fayemi, Gwamna Simon Lalong da Boss Mustapha.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Ɗaya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki

Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki

A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda gwamnatinsa a cikin kwana daya ta magance yajin aikin wata hudu da kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta taba yi.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba wurin bikin cikar Bishop Mathew Kukah shekaru 70 da haihuwa da aka yi a Cibiyar Kukah da ke Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Legit Hausa ta rahoto cewa jami'o'i a Najeriya sun fara yajin aiki tun watan Fabrairu kan rashin cika musu bukatunsu da gwamnatin tarayya ba ta yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel