Jerin Jihohin da Dole Atiku Ya Ci Zabe Kafin Ya Gaji Buhari a zaben 2023

Jerin Jihohin da Dole Atiku Ya Ci Zabe Kafin Ya Gaji Buhari a zaben 2023

Yayin da zaben 2023 ya karato, wani rahoton Thisday ya yi nazari kan damammaki da manyan ‘yan takaran shugaban kasa; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Bola Tinubu na APC da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya kamata su kama.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Akalla kwanaki 177 ne suka rage a kada kuri'u, rahoton ya nuna cewa, akwai bukatar sanin inda kowane dan takara zai fi karf da maida hankali domin lashe zabe.

A burin Atiku na gaje Buhari, an jero wasu jihohin da ya kamata ya ci zabe da kuma hasashen karfinsa a wasu jihohin.

Jihohin da Atiku zai lashe zabe ya gaji Buhari
Jerin Jihohin da Dole Atiku Ya Ci Zabe Kafin Ya Gaji Buhari a zaben 2023 | Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ga su kamar haka:

Jerin jihohin da dole ya kawo 60% na kuri'u

Jerin jihohiYiwuwar kawo 60% na kuri'u
1AdamawaAna kyautata zato
2TarabaAna kyautata zato
3BauchiZai yiwu
4BenueZai yiwu
5FilatoZai yiwu
6SokotoAna kyautata zato
7JigawaZai yiwu
8KatsinaAna kyautata zato
9KebbiZai yiwu
10DeltaAna kyautata zato
11EdoAna kyautata zato
12Akwa IbomAna kyautata zato
13BayelsaAna kyautata zato
14KadunaZai yiwu

Kara karanta wannan

Rikici Ya Tsananta: Butulci da Girman Kai Ba Zasu Kaika Ko Ina Ba, Wike Ya Caccaki Shugaban PDP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jerin jihohin da dole ya kawo 40% na kuri'u

Jerin jihohiYiwuwar kawo 40% na kuri'u
1LegasZai yiwu
2OgunZai yiwu
3OsunAna kyautata zato
4OyoAna kyautata zato
5KanoZai yiwu
6RibasZai yiwu
7Kuros RibaZai yiwu
8KogiZai yiwu
9KwaraZai yiwu
10NasarawaZai yiwu
11NejaZai yiwu
12FCTAna kyautata zato

Abin lura: Duk da cewa rahoton bai bayyana hasashen jihohin ba, Legit.ng ta yi la'akari da jihohin da Atiku ya fi samun karbuwa, don haka ta bayyana zato mai karfi ga Atiku ya iya kawo kuri'u masu gwabi daga jihohi kasancewarsu na PDP.

A bangare guda, jihohin dake karkashin APC na iya zame Atiku ciwon kai, don akwai yiwuwar ya kawo su, amma da sudin goshi.

Kara karanta wannan

Jerin Jihohin Da Ya Wajaba Tinubu Ya Ci Idan Yana Son Nasara A Zaben 2023

Jerin Jihohin Da Ya Wajaba Tinubu Ya Ci Idan Yana Son Nasara A Zaben 2023

A wani labarin, yayinda ake sauran kwanaki 177 zaben shugaban kasar Najeriya, wani rahoton jaridar ThisDay yayi hasashen jihohin da manyan takara uku ke bukatan ci.

Yan takaran sun hada da Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.

Rahoton ya yi bayanin jihohin da ya wajaba wanda ke son nasara cikin wadannan yan takara uku yayi nasara idan har yana non zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel