Jerin Jihohin Da Ya Wajaba Tinubu Ya Ci Idan Yana Son Nasara A Zaben 2023

Jerin Jihohin Da Ya Wajaba Tinubu Ya Ci Idan Yana Son Nasara A Zaben 2023

Yayinda ake kasa da sauran kwanaki 100 zaben shugaban kasar Najeriya, wani rahoton jaridar ThisDay yayi hasashen jihohin da manyan takara uku ke bukatan ci.

Yan takaran sun hada da Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.

Rahoton ya yi bayanin jihohin da ya wajaba wanda ke son nasara cikin wadannan yan takara uku yayi nasara idan har yana non zama shugaban kasa.

Game da Tinubu, rahoton ya lissafo jerin jihohin da ya wajaba ya samu kashi 60% da kuma 40% da kuma yiwuwan samun hakan.

Shettima
Jerin Jihohin Da Ya Wajaba Tinubu Ya Ci Idan Yana Son Nasara A Zaben 2023 Hoto: APC
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jerin jihohin da ya wajaba Tinubu ya samu akalla 60% idan yana son zama shugaba

Jihohin da Ya Wajaba Tinubu Yaci 60% Yiwuwan hakan
1LagosAna Sa rai
2OgunAna Sa rai
3OndoAna Sa rai
4OyoDa Yiwuwa (Sai Ya Dage)
5OsunDa Yiwuwa
6EkitiAna Sa rai
7KanoDa Yiwuwa (Kamar Wuya)
8KadunaDa Yiwuwa (Sai Ya Dage)
9KatsinaDa Yiwuwa (Sai Ya Dage)
10ZamfaraAna Sa rai
11BornoAna Sa rai
12YobeAna Sa rai

Jerin jihohin da ya wajaba Tinubu ya samu akalla 40% idan yana son zama shugaba

Jihohin da Ya Wajaba Tinubu Yaci 40% Yiwuwan hakan
1SokotoAna Sa rai
2KebbiAna Sa rai
3JigawaDa Yiwuwa
4BenueDa Yiwuwa (Kamar Wuya)
5KogiAna Sa rai
6NigerAna Sa rai
7KwaraDa Yiwuwa
8PlateauDa Yiwuwa
9FCTDa Yiwuwa

Abin lura: Mafi akasarin jihohin dake karkashin mulkin APC yanzu ake sa ran Tinubu zai samu rinjaye.

Hakazalika Mafi akasarin jihohin dake karkashin mulkin PDP yanzu ake sa ran Tinubu sai ya yi da gaske

Asali: Legit.ng

Online view pixel