Komawar Shekarau PDP: Wasu Yan Majalisar Shura Da Manyan Yan Siyasa Sunyi Taro, Sun Bayyana Matsayarsu

Komawar Shekarau PDP: Wasu Yan Majalisar Shura Da Manyan Yan Siyasa Sunyi Taro, Sun Bayyana Matsayarsu

  • Wasu yan siyasa da kuma mambobin majalisar Shura da ke bawa Sanata Ibrahim Shekarau shawara sun ce ba za su bi shi zuwa PDP ba
  • A baya-bayan nan Sanata Shekarau ya fice daga jam'iyyar NNPP ya koma PDP kan cewa ba a yi masa adalci ba da magoya bayansa da suka dawo NNPP
  • Sai dai wasu cikin wadanda suka shigo NNPP din tare da Shekarau sun yi taro sun kuma fitar da takardar cewa su a NNPP za su cigaba da zama sun kuma bada dalilinsu

Kano - Fiye da yan siyasa 40 da suka koma jam'iyyar NNPP tare da Sanata Ibrahim Shekarau sun yanke shawarar za su cigaba da zama a jam'iyyar ta goyon bayanta a babban zaben 2023, Daily Nigerian ta rahoto.

Taron yan siyasan Kano
Komawar Shekarau PDP: Wasu Yan Majalisar Shura Da Manyan Yan Siyasa Sunyi Taro, Sun Bayyana Matsayarsu. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

Da ya ke karanto sakon karshen taro a madadin yan siyasa 45 bayan taronsu, mamba mai wakiltar Karaye/Rogo, Haruna Dederi, ya shi mambobin 45 da suka rattaba hannu kan sakon karshen taron, sun yanke shawarar cigaba da zama a NNPP su yi zabensu.

Dalilin da yasa za mu cigaba da zama a NNPP - Dederi

Mista Dederi, wanda lauya ne ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A yanzu babu wata jam'iyya da ta fi NNPP magoya baya da shugabanni masu hangen nesa. Wannan gaskiya ne da aka sani a ko ina. Muna kira ga mutanen mu su cigaba da bamu hadin kai don mu sauya akalar jihar mu don cigaba mutanen da ceto kasar mu daga rushe wa.
"Mun kuma yarda cewa kowane dan kasa na da ikon yin zabinsa ko canja wadanda ya ke mu'amula da su kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulkin kasa."

Lauyan ya kara da cewa sun shiga NNPP ne saboda manufofinta da ya ce sun bada muhimmanci wurin warware matsalolin kasa.

Ya yi kira ga magoya bayan yan siyasa 45 din da suka rattaba hannu kan sanarwar bayan taron su kwantar da hankulansu su cigaba da bin doka, ya tabbatar musu ba za su basu kunya ba a siyasance.

Wadanda suka halarci taron

Taron ya samu halarcin dan takarar gwamna na NNPP, Abba Yusuf; dan takarar mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam; dan takarar sanata (Kano South) Kawu Sumaila; tsohon kakakin majalisar dokokin Kano, Gambo Sallau da mamba mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum.

Saura sun hada da shugaban fadar ma'aikatan Gwamna Abdullahi Ganduje, Ali Makoda da tsohon kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Nura Dankadai.

Kwankwaso Ya Bude Baki Kan Gaskiyar Abin da Ya Faru Da Su da Shekarau a NNPP

A wani rahoton, an yi hira da Rabiu Musa Kwankwaso a VOA Hausa inda ya yi bayanin abin da ya jawo Ibrahim Shekarau ya bar NNPP da sunan ba ayi masa adalci ba.

Mai neman takarar shugaban kasar a NNPP ya bayyana cewa kurewar lokaci ya hana a ba ‘yan bangaren Sanata Shekarau takarar kujeru da-dama a jam’iyyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel