Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Yara Mabarata Sun Tara Masa Kudin Siyan Abinci Bayan Ya ce Yana Jin Yunwa

Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Yara Mabarata Sun Tara Masa Kudin Siyan Abinci Bayan Ya ce Yana Jin Yunwa

  • Wani bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta ya nuna wani abin sha'awa da ya faru lokacin da matasa suka taimaki matashi da kudi
  • Matashin ya sanar da yaran cewa yana jin yunwa ne kuma yaran masu tausayi suka tara masa kudi ya siya abinci
  • A martanin da suka yi game da bidiyon, masu amfani da dandalin sada zumunta sun yaba da kirkin yaran

Wani mutum mai suna King Principal ya bayyana karamcin da wasu mabarata da ya taba taimako suka masa.

Principal ya bayyana cewa ya saba bawa yaran kyautan kudi duk lokacin da suka taho wurinsa suna bara.

Mabaraci Da Yara
Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Yara Mabarata Sun Tara Masa Kudin Siyan Abinci Bayan Ya ce Yana Jin Yunwa. Hoto: @King Principal
Asali: UGC

Amma, a wata rana, Prince ya ce yunwa ta kama shi kuma ya sanar da yaran halin da ya ke ciki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Wata Kabila A Duniya Ta Shafe, Mutum 1 Da Ya Rage Ya Koma Ga Allah

Ba tare da bata lokaci ba, suka tattara kansu suka masa karo-karon kudi suka mika masa.

Prince ya karbi kudin da murmushi a fuskansa, ya kirga ya gano N280 suka tara masa.

Prince ya dubi yaran cike da mamaki a fuskarsa ya musu godiya kwarai da gaske.

Amma daga bisani ya canja ra'ayinsa ya mayar musu da kudin.

Da ya ke wallafa bidiyon a TikTok, ya ce:

"Na saba ba su kudi amma yau sun yi min karo-karo saboda na fada musu ina jin yunwa."

Masu amfani da dandalin sada zumunta sun yi martani

@user7098patrix ya ce:

"Sun nuna maka ainihin ma'anar abokantaka."

@princechristopherrev ya rubuta:

"Wasu da dama ba su san abin da wannan zai yi ga rayuwar yaran ba. Rayuwarsa za ta canja. Ka kyauta."

@diibawal ya yi tsokaci da cewa:

"Allah kadai zai saka maka da iyalanka amma yaran nan fa suna da kudi. Dubi N20 masu yawa."

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

@deniniscu55 ya ce:

"Yara masu kudi! Ji yadda suke fito da kudinsu."

Kalli bidiyon a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel