Sanatan Daura Ya Karbe Ofishin Yakin Neman Zaben da aka fara ba Buhari a 2002

Sanatan Daura Ya Karbe Ofishin Yakin Neman Zaben da aka fara ba Buhari a 2002

  • Sanata Ahmad Babba-Kaita ya saye wani ofishin kungiyar TBO ta magoya bayan Muhammadu Buhari a garin Daura
  • Babba-Kaita wanda shi ne Sanata mai wakiltar Arewacin Katsina ya sha alwashin karya APC tun da ya bar Jam’iyyar
  • Ofishin da ‘Yan TBO ta dade tana amfani da shi ya zama sabon sakatariyar jam’iyyar PDP a karamar hukumar Daura

Katsina - Sanata mai wakiltar Arewacin jihar Katsina, Ahmad Babba-Kaita ya dage a kan bakarsa na ganin bayan jam’iyyar APC a Katsina a zabe mai zuwa.

A wani rahoto da Premium Times ta wallafa a farkon makon nan, an ji Sanata Ahmad Babba-Kaita ya karbe ofishin yakin neman zaben Muhammadu Buhari.

Wannan ofishin kamfe yana nan a garin Daura, tun shekarar 2002 kungiyar The Buhari Organisation (TBO) ta mallaki ofishin da Buhari ya soma siyasa.

Kara karanta wannan

Yadda Malam Shekarau ya Canza Jam’iyya Sau 4 a Shekaru 8 Daga 2014 Zuwa 2022

Ginin APC ya zama na PDP

Har zuwa makon da ya wuce, kungiyar ta The Buhari Organisation watau TBO ta ke amfani da ofishin, sai kwatsam aka ji Sanata Babba-Kaita ya saye ginin.

Rahoton yace shugabannin jam’iyyar APC na garin Daura sun dade suna amfani da wannan ofishi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da sayen ofishin yakin neman zaben, Sanatan ya mallaka shi ga jam’iyyar hamayya ta PDP, ya zama babban ofishin kamfe na APC a karamar hukumar Daura.

Sanatan Daura
Sanata Ahmad Babba Kaita da Atiku Abubakar Hoto: @ahmad.babbakaita
Asali: Facebook

Tarihin ofishin kamfe

Asali tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya, Hon. Salisu Ado ne ya mallaki wannan ginin bene, ya kuma kyale ayi amfani da shi ba tare da an biya kudi haya ba.

Da ‘dan siyasar ya rasu sai ginin ya zama na marayu da suka nemi a rika biyansu kudin amfani da shi, da dawainiyar ofishin ya gagara, dole sai aka saida shi.

Kara karanta wannan

PDP ta Karbi Shekarau, Mai ba Buhari Shawara Ya Yi Hasashen Wanda Zai Ci Zaben Kano

Wani wanda ya san abin da ya faru, ya shaidawa jaridar cewa an saidawa Ahmad Babba Kaita ofishin bayan an yi shekaru uku ‘Yan TBO ba su biya haya ba.

Daga baya kenan...

Wani daga cikin jagororin kungiyar TBO a garin Daura, ya bayyana cewa sun ci riba da ofishin tun da dai Muhammadu Buhari ya zama shugaban Najeriya.

Wannan mutumi wanda yana cikin masu ba Gwamna Aminu Bello Masari shawara, ya nuna saidawa PDP ofishin da aka yi bai nufin wata gazawa gare su.

‘Dan Majalisar Daura zai bar APC?

Kwanaki an ji labari Fatuhu Muhammad ya bada sanarwar barin APC saboda zagin mahaifinsa, jiya ‘dan majalisar na Daura/Sandamu/Mai’adua ya canza shawara.

Tun bayan zaben fitar da gwani ake rigima a mazabar Daura, abin ta kai Hon. Fatuhu Muhammed yace ya bar APC, a jiya aka ji cewa ya janye matakin da ya dauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel