Yadda Gwamnatin Wike Ta Garmake Otal da Mashayar Jigon Siyasar Dan Takarar PDP Atiku
- Gwamnatin jihar Ribas ta garkame wasu wuraren kasuwanci mallakin dan tsagin Atiku a jam'iyyar PDP
- Jami'an tsaro sun dura wasu otal, mashaya da gidan mai mallakin Hon Austin Opara, an kame wasu ma'aikata
- Ana kai ruwa rana tsakanin Atiku da gwamna Wike na Ribas, majiya na ganin akwai batun siyasa a wannan kame
Fatakwal, jihar Ribas - Wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa, jami'an tsaro da sanyin safiyar yau Juma'a suka garkame otal da matasha, gidan mai mallakin wani jigon siyasar jam'iyyar PDP.
An garkame otal da mashayan ne da ke a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas saboda gudanar wani taro ba bisa ka'ida ba.
Hakazalika, an kame wasu mutane da ke da hannu da taron, ciki har da ma'aikatan da ke aiki a wurin.
Wuraren da gwamnatin ta garkame su ne; Preray Hotel da ke Eagle Island, Mashayar Priscy a Elekahia da gidan man Mega Tool da ke kan titin Ojoto a Diobu, duk dai a babban birnin na jihar Ribas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A baya, gwamna Nyesom Wike ya yada batun cewa, ana zargin wasu ‘yan siyasa na daukar tsageru da matsafa aiki domin dagula zaman lafiyar jihar yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa.
Duk da cewa rahoton da muka samo bai bayyana boyayyen dalilin wannan kame ba, hasashen majiya na cewa, akwai batu na siyasa game da hakan.
Waye mai wannan wuri da aka garkame?
Rahoton ya ce, wuraren da aka garkame mallakin wani na hannun daman tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai ne, Hon Austin Opara.
Opara, wanda a baya na hannun dana Wike ne, a yanzu ba sa ga maciji tun bayan da ya nuna goton bayansa ga takarar shugaban kasa ta Atiku Abubakar, mai rike da turar PDP.
Wata sanarwa da hadimin Wike kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri ya fitar ta ce gwamnan na sane da cewa masu otal da wuraren shakatawa na ba 'yan siyasa wuraren ga 'yan siyasar da ke tara tsageru da sunan taron siyasa.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Haka nan, ba za mu kyale wata jam’iyyar siyasa ba, PDP, PDP ko SDP, ta yi barazana ga rayuka da dukiyoyin al'umma a lokacin gangamin yakin neman zabe ba ta hanyar tada hankalin jama'a, ko amfani da tsageru ko 'yan daba ba.
“Don haka, mun ankarar da jami’an tsaro domin bin diddigin irin wadannan bata-garin ‘yan siyasa da shugabannin jam’iyyun siyasa tare da dakatar da su daga yunkurinsu ta hanyar amfani da cikakken ikon doka."
A bangare guda, Wike ya yi gargadin rusa duk wani otal ko wurin shakatawa da ke da irin wadannan miyagun siyasa da ayyukansu.
Majiya ta tuntubi kwamishinan 'yan sandan jihar, Friday Eboka domin jin ta bakinsa, amma ba a samu jin wani batu mai karfafa wannan lamari ba.
Rikicin Atiku Da Wike: "Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi
A wani labarin, daya cikin wadanda aka kafa jam'iyyar PDP da su kuma mamba na kwamitin amintattu, Cif Bode George, ya ce rikicin cikin gidan na jam'iyyar na damunsa, yana mai cewa shedan ya ratsa jam'iyyar, Daily Trust ta rahoto.
Jam'iyyar ta rika fuskantar rikici tun bayan nasarar da Atiku Abubakar ya samu a matsayin dan takarar shugaban kasa, bayan kayar da Nyesom Wike na Jihar Rivers.
Jiga-jigan jam'iyyar na PDP da dama sun bada shawarar Wike ya zama mataimakin Atiku amma tsohon mataimakin shugaban kasar ya zabi gwamnan Jihar Delta, Dr Ifeanyi Okowa. Rikicin jam'iyyar ya kara rincabewa bayan hakan.
Asali: Legit.ng