Tawagar Gwamna Wike da Ta Atiku Sun Shigawa Ganawar Sirri Don Neman Sulhu

Tawagar Gwamna Wike da Ta Atiku Sun Shigawa Ganawar Sirri Don Neman Sulhu

  • Rahoton da muke samu daga jihar Ribas ya bayyana cewa, gwamnan jihar Adamawa ya jagoranci tawagar tattaunawa da 'yan tsagin Wike
  • Ana zaman doya da manja tsakaninAtiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a PDP da gwamnan jihar Ribas Wike
  • Gwamna Wike ya bayyana matsayarsa cewa, ba zai yiwa kowace jam'iyya dariya ba wajen kare jiharsa daga matsaloli

Fatakwal, jihar Ribas - Daga karshe dai sashen gwamnan Ribas Nyesom Wike da na dan takarar shugaban kasan jam’iyyar PDP mai adawa, Atiku Abubakar sun gana a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas domin dinke baraka.

A cewar rahoton jaridar The Nation, ganawar ta samu halartar gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri a matsayin jagoran tawagar Atiku da, inda suka dira fadar gwamna Wike a madadin Atiku.

Yanzun nan ake zaman sulhu tsakanin tawagar Wike da ta Atiku
Tawagar gwamna Wike da ta Atiku sun shigawa ganawar sirri don neman sulhu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Tun bayan kammala zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP na dan takarar shugaban kasa Wike da Atiku ke zaman doya da manja saboda wasu mabambantan ra'ayoyi da ke tsakani.

Kara karanta wannan

Siyasa ba gaba: Gwamna Wike ya garkame wuraren kasuwanci 3 na dan a mutun Atiku a Ribas

Atiku ya kara tunzura Wike tun bayan da ya zabi gwamnan Delta, Okowa a matsayin abokin gami a takararsa, lamarin da ya fusata gwamnan da ma 'yan a mutunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kallama tattaunawa

Wani bidiyo da wakilinmu ya gano daga jaridar Vanguard ya nuna lokacin da wadanda suka halarci zaman ke fitowa.

Fintiri ya shaidawa manema labarai cewa, nan ba da jimawa za a samu daidaito tsakanin Atiku da Wike, kana jam'iyya ta zauna lafiya.

Sai dai, wata majiyar cikin taron ta shaidawa Vanguard cewa, har yanzu dai ba a samu wata matsaya ba, kuma akwai dambarwar da ke tsakani duk da wannan zama.

Yadda Gwamnatin Wike Ta Garmake Otal da Mashayar Jigon Siyasar Dan Takarar PDP Atiku

A wani labarin kuma, wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa, jami'an tsaro da sanyin safiyar yau Juma'a suka garkame otal da matasha, gidan mai mallakin wani jigon siyasar jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Matasa Suka Wanke Hanyar Da Atiku Ya Bi Bayan Ya Ziyarci Mahaifarsa Da Ruwa Da Sabulu

An garkame otal da mashayan ne da ke a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas saboda gudanar wani taro ba bisa ka'ida ba.

Hakazalika, an kame wasu mutane da ke da hannu da taron, ciki har da ma'aikatan da ke aiki a wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel