Rikicin Atiku Da Wike: "Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi

Rikicin Atiku Da Wike: "Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi

  • Cif Olabode George, dattijon kasa ne, kuma tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na kasa
  • Yayin da ya ke tsokaci kan rikicin da ke tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike ya ce shedan ya karbe shugabancin jam'iyyar ta PDP
  • Rikicin cikin gida da ke faruwa a jam'iyyar ta PDP mai hamayya yana ta raba kan yan jam'iyyar a watannin baya-bayan nan gabanin zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Daya cikin wadanda aka kafa jam'iyyar PDP da su kuma mamba na kwamitin amintattu, Cif Bode George, ya ce rikicin cikin gidan na jam'iyyar na damunsa, yana mai cewa shedan ya ratsa jam'iyyar, Daily Trust ta rahoto.

Jam'iyyar ta rika fuskantar rikici tun bayan nasarar da Atiku Abubakar ya samu a matsayin dan takarar shugaban kasa, bayan kayar da Nyesom Wike na Jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Mukamai 15 Masu Gwabi Da El-Rufai Da APC Ta Arewa Maso Yamma Suka Nema Daga Wurin Tinubu

Atiku da Wike
Rikicin Atiku Da Wike: "Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi. Hoto: Photo credit: PDP Governors in Action.
Asali: Facebook

Jiga-Jigan jam'iyyar sun yi kokarin yin sulhu

Jiga-jigan jam'iyyar na PDP da dama sun bada shawarar Wike ya zama mataimakin Atiku amma tsohon mataimakin shugaban kasar ya zabi gwamnan Jihar Delta, Dr Ifeanyi Okowa. Rikicin jam'iyyar ya kara rincabewa bayan hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a wani hira da aka yi da shi a Channels TV a shirin Politics Today, George ya bayyana cewa jam'iyyar za ta iya magance rikicin ta tunkari zaben 2023, Jaridar The Sun ta kara.

Ya ce:

"Ba ni kadai abin ke damu ba, yana damun mambobi, jiga-jigai da dattawan jam'iyyar. Tamkar wani irin shedani ya shigo jam'iyyar mu ne. Amma bari in fada maka wani abu. Jam'iyyar mu za ta iya warware matsalolin.
"A jam'iyyar mu, muna da shugabanni kwararru; mun da shugabanni jajirtattu; muna da shugabanni masu kishin jam'iyya da za su zauna su warware matsalar baki daya. Kuma gashi muna da makwonni kafin a fara kamfen.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Atiku, Tinubu Shima Yana Zawarcin Shekarau, Za Su Gana Ranar Laraba

"Warware matsalar wani mizani ne da zai nuna irin cigaban da jam'iyyar ta samu, idan baka iya warware matsaloli ba, toh ba baka cika jam'iyya ba. Muna da mutanen da suka fara aiki kan lamarin, saura mataki daya mu tsallake kuma za mu zama cikin shiri don fafatawa a zaben 2023."

2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda

A bangare guda, gwamnonin jam'iyyar PDP da ke biyaya ga gwamnan Rivers, Nyesom Wike, sun bada wasu sharruda ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, kafin su mara masa baya a zaben 2023, kamar yadda aka rahoto.

A cewar Daily Independent, gwamnonin za su hadu da Atiku a karshen mako don tattaunawa kan matsalolin da ke adabar jam'iyyar.

Jaridar ta rahoto cewa daya daga cikin mambobin tawagar Gwamna Wike yana cewa duk ma abin da ya faru, sun amince babu wanda zai fita daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel