Kaduna: Dakarun Soji Sun yi Arangama da 'Yan Bindiga, Sun Kwato Mai Jego Da Jaririnta

Kaduna: Dakarun Soji Sun yi Arangama da 'Yan Bindiga, Sun Kwato Mai Jego Da Jaririnta

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da ceto wata mata mai jego da jinjirarta da sojoji suka yi a babbar hanyar Zaria zuwa Kano daga hannun 'yan bindiga
  • Kamar yadda kwamishinan tssaron cikin gida, Samuel Aruwan ya bayyana, sojoji sun ci karo da 'yan bindiga suna niyyar hijira a Ungwan Namama
  • Yace sun bude musu wuta tare da kwace mutum uku da suka yi garkuwa da su sannan suka samo wasu dabbobin sata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna tace hukumomi sun ceto wata mai jego da wasu mutum biyu a wuraren Ungwan Namama, a kan babban hanyar Zaria zuwa Kano, jaridar The Cable ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, a wata takardar da ya fitar ranar Alhamis, yace dakarun sun ci karo da 'yan bindigan dake hijira a yankin kuma suka yi musu ruwan wuta, lamarin da ya tirsasa su barin mutum uku da suka sato sannan suka tsere.

Kara karanta wannan

Mazauna a Kaduna sun fusata, sun sheke wata wata mai boye 'yan bindiga a gidanta

Taswirar jihar Kaduna
Kaduna: Dakarun Soji Sun yi Arangama da 'Yan Bindiga, Sun Kwato Mai Jego Da Jaririnta. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Wadanda aka ceto an gano sunayensu da Abdullahi Lawal, Sadiya Salimanu da Fatima Salimanu (jinjira mai wata goma). Bincike ya bayyana cewa, an sace su ne a jihar da ke da kusanci da Kaduna," yace.

Aruwan ya kara da cewa, dakarun sun samo shanun sata daga 'yan bindigan da suka hada da sa daya sai tumaki takwas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta rahoto cewa, yace gwamnatin jihar na mika godiya ga sojojin kan kokarinsu wurin ceto wadanda aka sace.

Ya kara da cewa, wadanda aka ceto din an mika su ga iyalansu yayin da dabbobin satan ke hannun hukumomin yankin don mika su ga masu su.

Yadda Jami’an ’Yan Sanda Suka Ceto Wasu Mutanen da Aka Yi Garkuwa Dasu a Jihar Kwara

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta ceto mutum hudu daga cikin mutane shida da aka sace a babbar hanyar Obbo-Ile da Osi a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto mutum 4 daga hannun miyagun 'yan bindiga a wata jiha

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Okasanmi Ajayi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata 16 ga watan Agusta a Ilorin, Premium Times ta ruwaito.

Ya bayyana cewa, jim kadan bayan samun labarin abin da ya faru, jami'an 'yan sanda, 'yan banga da mafarauta sun dura wurin da lamarin ya faru domin gano tushen lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel