‘Yan Takara Sun Dauko ta da zafi, Sun yi wa Atiku Abubakar alkawarin Kuri’a Miliyan 20

‘Yan Takara Sun Dauko ta da zafi, Sun yi wa Atiku Abubakar alkawarin Kuri’a Miliyan 20

  • Wadanda suka shiga zaben neman tikitin Majalisa za su marawa Atiku Abubakar baya a 2023
  • Kungiyar ‘Yan takaran Majalisar Tarayyan na PDP sun yi wa Atiku alkawarin kuri’u miliyan 20
  • A tarihi ba a taba samun ‘Dan takaran Jam’iyyar adawa da ya samu fiye da kuri’a miliyan 12 ba

Abuja - Kungiyar masu harin takarar majalisar wakilan tarayya a karkashin jam’iyyar APC sun sha alwashin taimakawa Atiku Abubakar a zaben 2023.

Rahoton da muka samu daga Daily Trust ya nuna cewa masu neman kujerar majalisar tarayyar sun yi alkawari za su ba Atiku Abubakar kuri’u miliyan 20.

Wannan kungiya ta kunshi ‘yan siyasa fiye da 1000 wanda suka shiga zaben fitar da gwanin majalisar tarayya a inuwar PDP a fadin mazabun da ke kasar nan.

Kara karanta wannan

Rikici: Kiristocin APC a Arewa sun ta da hankali, dole a kwace tikitin Shettima a ba su

Shugaban wannan kungiya ta ‘yan adawar siyasa, Mohammed Danjuma ya fitar da jawabi na musamman, yana magana a kan takarar Alhaji Atiku Abubakar.

Blueprint ta rahoto Danjuma yana mai cewa nasarar Atiku Abubakar da PDP a zaben shugaban kasa na 2023, tamkar nasarar duk wani mutumin Najeriya ne.

Danjuma ya nuna su na sa ran cewa jam’iyyar hamayyar za tayi waje da gwamnatin APC a badi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A karshen wannan jawabi da ya shiga hannun manema labarai, shugaban kungiyar masu neman takaran yace gwamnatin PDP ce za ta iya gyara tattalin kasa.

Atiku
Atiku da wasu 'Yan PDP daga Kogi Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

“Mu na sa ran samun nasara, ta haka ne kurum za a iya ceto kasar nan daga mummunan jagorancin da gwamnatin nan take yi.
Domin ceto tattalin arzikin kasar mu daga rikon APC da gwamnatinta.” - Mohammed Danjuma

Kara karanta wannan

Daga Fitowa daga Kurkuku, Dariye Zai Shiga Takara, Ana Masa Harin Kujerar Sanata

Hakan zai yiwu a 2023?

Da Atiku Abubakar ya nemi mulki a zaben 2019, ya tashi da kuri’u miliyan 11.2 ne. Wannan ne mafi yawan kuri’un da ya taba samu a takarar shugaban kasa.

A zaben 2007 da Atiku ya yi takara a ACN, ya samu kuri’a miliyan 2.6 ne, abin da bai kai 8%. Tun bayan 2011, babu ‘dan takaran da ya samu kuri’u miliyan 20.

Siyasar Katsina

A jihar shugaban kasa, an ji labari Jam’iyyar APC ta canza ‘Dan takarar Mataimakin Gwamnan Katsina, ta bada sunan Kwamishinan tattali, Faruq Lawal Jobe.

Jobe wanda Kwamishina mai-ci ne ya canji Yusuf Aliyu Musawa a tikitin jam’iyyar, ya zama abokin takarar Dr. Dikko Radda, za su yaki PDP, NNPP, da SDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel