Ana Shirin Shiga Kamfe, APC ta Canza Tikitin ‘Yan takarar Gwamnan jihar Katsina

Ana Shirin Shiga Kamfe, APC ta Canza Tikitin ‘Yan takarar Gwamnan jihar Katsina

  • ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a APC, ya canza sunan wanda zai zama abokin takararsa
  • Dr. Dikko Umar Radda ya dauko Hon. Faruq Lawal Jobe ya zama ‘dan takarar mataimakin Gwamna
  • Faruq Lawal Jobe wanda Kwamishina mai-ci ne ya canji Yusuf Aliyu Musawa a tikitin jam’iyyar

Katsina - A ranar Alhamis, 11 ga watan Agusta 2022, muka samu labari cewa Dr. Dikko Umar Radda, ya zabi wanda zai zama abokin takararsa.

Daily Trust ta rahoto cewa Dikko Umar Radda wanda zai yi takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC ya dauki Faruk Lawal Jobe.

Da farko Dr. Dikko Radda ya bada sunan Yusuf Aliyu Musawa ne a matsayin wanda zai zama ‘dan takarar mataimakin gwamna a APC a zaben 2023.

Wani jawabi da ya fito daga bakin shugaban kungiyar Gwagware Media Organisation a Katsina, Abdulkadir Ahmed ya tabbatar da wannan canji a APC.

Kara karanta wannan

Kaduna 2023: Tsohon Shugaban Kungiyar yan Kudancin Kaduna Ya Zama Dan Takarar Gwamna A Jam’iyyar Labour Party

Rahoton yace Alhaji Yusuf Aliyu Musawa ya amince ya janye takararsa bayan ya tattauna da jagarori da masu da tsaki a jam’iyyar APC na Katsina.

Wanda aka zaba yanzu Faruk Lawal Jobe yana cikin abokan hamayyar Dikko Radda a zaben fitar da gwani da jam’iyya ta shirya domin tsaida ‘dan takara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan takarar Gwamnan jihar Katsina
Dikko Umaru Radda tare da Hon. Faruk Lawal Hoto: GwagwareMediaReporters
Asali: Facebook

A karshe tsohon shugaban hukumar na SMEDAN ya samu tikiti, ya doke Jobe da wasu ‘yan takaran. Katsina Post ta tabbatar da wannan a rahoto jiya.

Wanene Faruk Lawal Jobe?

Faruk Lawal Jobe shi ne yake rike da kwamshinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattali a jihar Katsina, ya koma kan kujerarsa ne bayan ya rasa takara.

Masu fashin bakin harkar siyasar Katsina su na ganin cewa Jobe yana cikin na hannun daman Gwamna Aminu Bello Masari, wanda ake rufe kofa da su.

Kara karanta wannan

Atiku v Wike: Barakar Cikin PDP Ta Yi Zurfi, Jam’iyya Ta Gagara Yin Muhimmin Taro

Da za a shiga zaben fitar da ‘dan takara, Jobe ya ajiye kujerarsa kamar yadda doka tayi umarni. Bayan ya sha kasa sai aka ji gwamna ya sake dawo da shi.

Rikicin PDP a matakin kasa

Ku na da labari cewa jagororin PDP su na neman yadda za a lallabi Nyesom Wike, amma Gwamnan ya fara watsi da jam’iyyarsa, yana bin Jiga-jigan APC.

Abin ya kai Sakataren PDP a Najeriya, Sanata Samuel Anyanwu ya bada sanarwa cewa zaman NEC da aka shirya aba zai yiwu ba, sai wani lokaci a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel