‘Yan Majalisa Sun Dage Kan Batun Tsige Shugaban kasa, Sun Ce ‘babu ja da baya’
- Wasu Sanatocin jam’iyyar hamayya sun nuna maganar tsige shugaban kasa tana nan fa har gobe
- ‘Yan majalisar dattawan sun musanya rade-radin cewa Sanatoci sun ajiye maganar a gefe
- Mai magana da yawun Sanatoci yace ba su san da sauke Mai girma Muhammadu Buhari ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - ‘Ya ‘yan jam’iyyar adawa a majalisar tarayya sun ce yunkurin tsige shugaban Najeriya, Mai girma Muhammadu Buhari tana nan, ba su fasa ba.
Muddin shugaban kasar ya gagara shawo kan matsalar tsaro, ‘yan majalisar sun ce ba za su fasa tsige shi ba. Punch ta kawo rahoton nan a ranar Litinin.
Sanata Francis Fadahunsi mai wakiltar gabashin Osun a inuwar PDP yace ba gaskiya ba ne a rika cewa sun ja baya daga yunkurin sauke shugaban kasar.
Fadahunsi ya tabbatar da cewa Sanatocin adawa ba su janye wannan yunkuri da aka dauko ba. Sanatan yace har ‘yan majalisar Arewa na goyon bayansu.
Wannan shi ne maganar da Sanata Danjuma La’ah ya yi a lokacin da Punch tayi hira da shi, yace wa’adin da suka ba gwamnati na makonni shida na nan.
Duk da an je hutu, batun na nan
Wani ‘dan adawa a majalisar dattawa, Nicholas Tofowomo ya shaidawa jaridar cewa iyakar saninsa shi ne har yanzu maganar tsige shugaban kasa na nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanata Nicholas Tofowomo yace da an dakatar da yunkurin, da shugaban marasa rinjaye ya sanar da su duk da cewa yanzu ‘yan majalisar sun tafi hutu.
Sanatan na jihar Ondo yake cewa kafin a hakura da maganar, sai an tattauna da su, kuma a iyaka saninsa, har zuwa yanzu ba ayi hakan a majalisar ba.
Ba mu san ana yi ba - Majalisa
Amma mai magana da yawun bakin majalisar dattawan, Ajibola Bashiru ya bayyana cewa a hukumance, babu wani yunkurin tsige shugaban kasa a gabansu.
Rashin Tsaro: Za Mu Raba Lawan Da Kujeransa Idan Ya Kawo Mana Cikas Wurin Tsige Buhari, In Ji Sanatan Najeriya
Sanata Ajibola Bashiru yace bai da masaniya a kan kudirin tsige shugaban kasa a majalisar dattawa, domin za a fara yunkurin ne ta hanyar gabatar da kudiri.
A cewar Bashiru, ficewar da Sanatocin PDP suka yi daga majalisa a makon da ya wuce bayan soma maganar, bai nufin za a fara shirin tsige shugaban Najeriya.
Me mutanen Facebook ke fada?
Kwanaki muka zo da rahoto na musamman cewa wasu daga cikin masu amfani da dandalin Facebook sun karbi kiran tsige shugaban kasa a majalisar dattawa.
Mafi yawan masu magana sun gamsu a tunbuke Muhammadu Buhari saboda matsalar rashin tsaro a kasa, wanda yanzu har a garin Abuja ana wayyo Allah.
Asali: Legit.ng