Tashin hankali: Yadda matar aure tayi mutuwar farat daya a ƙuryar ɗakin kishiyarta

Tashin hankali: Yadda matar aure tayi mutuwar farat daya a ƙuryar ɗakin kishiyarta

  • Tashin hankali da alhini sun ziyarci iyalan Malam Musa, mazauna garin Zaria sakamakon mutuwar daya daga cikin matansa uku
  • Kamar yadda aka gano, amaryarsa Gambo ta rasu a dakin uwargidanta yayin da ake tsaka da hira, kwatsam rai yayi halinsa
  • Bincike ya tabbatar da cewa Gambo na fama da ciwon zuciya, lamarin da yasa ake tsammanin shi ya kawo mutuwarta farat daya

Zaria, Kaduna - Iyalan Malam Musa, mazauna Zaria a jihar Kaduna, sun fada tsananin tashin hankali da alhini sakamakon rasuwar farat daya da amaryarsa mai suna Gambo tayi.

Bayanai suna tabbatar da cewa, Gambo ta ziyarci kishiyoyinta biyu dake gida daya a wata sanyin safiyar Juma'a.

Taswirar jihar Kaduna
Tashin hankali: Yadda matar aure tayi mutuwar farat daya a ƙuryar ɗakin kishiyarta. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta Dunga Sharban Kuka Wiwi Tare Da Nuna Tirjiya A Wajen Baikonta Ya Haddasa Cece-kuce

Duk da ba wata jituwa ke tsakaninsu da kishiyoyin ba, sun zauna suna taba hira inda suke jiran dawowar mijinsu wanda yayi balaguro.

An kawo wa Gambo abinci amma tace ba za ta ci ba saboda ta kira mijinsu a waya tace masa tana bukatar cin gurasa, wacce yayi alkawarin taho mata da ita idan zai shigo gidan.

Kamar yadda uwargida Fati ta bayyanawa Legit.ng:

"Muna tsaka da hira kawai Gambo ta fado daga kan kujerar da take zaune a kai, sai jikina. Cike da tashin hankali nace me ke faruwa Gambo? Amma shiru, tambayar da har yau bata amsa min ba kenan.
"Tuni na fasa ihu tare da fita na kira makwabta. Duk wanda ya taba Gambo sai yace ai rai ne yayi halinsa. Haka muka dinga kuka cike da tashin hankali."

Bayan isowar Malam Musa ne ya tarar da wannan lamarin inda ya gigice tare da fita hayyacinsa. An yi wa Gambo jana'iza kamar yadda addinin Islama ya tanadar tare da kai ta gidanta na gaskiya. Bayanai daga bakin mijin Gambo da 'yan uwanta na kusa sun tabbatar da cewa tana fama da ciwon zuciya, lamarin da yasa aka karkata tsammanin cewa zuciyar ce tayi ajalinta.

Kara karanta wannan

Mansurah ga Tinubu: Zan yi maka kamfen da jinina, kyauta, in ka ceto fasinjojin jirgin kasan Abj-Kd

Bidiyo: An kwantar da 'dan siyasa a asibiti bayan ya sha gurbattacen ruwa don birge jama'arsa

A wani labari na daban, babban ministan Punjab na Indiya, Bhagwant Mann, yana kwance magashiyyan a asibiti bayan ya sha gurbataccen ruwa daga wani kogi domin tabbatarwa da jama'a cewa ruwan tsaftatacce ne.

A wani bidiyo, an ga Mann ya debi ruwan a kofin gilas daga kogin kuma da kwankwade shi yayin da magoya bayansa suke masa ihu da yabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel