Zabo abokin gami Musulmi: Kwakwalwarsa ta daina aiki, Atiku ya caccaki Tinubu

Zabo abokin gami Musulmi: Kwakwalwarsa ta daina aiki, Atiku ya caccaki Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake mayar wa abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC raddi kan wasu batutuwa
  • Atiku ya yi ikirarin cewa, Tinubu ya so yin takarar mataimakin shugaban kasa da shi a baya a jam’iyyar Action Congress, amma ya ki, duba da yadda tsarin siyasar addini a Najeriya
  • Batu dai ya yi tsami tsakanin Tinubu da Atiku, inda Atiku ya ce sam kwakwalwar Tinubu ta daina aiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake caccakar abokin hamayyarsa Bola Tinubu na jam’iyyar APC.

Atiku ya caccaki Tinubu kan ikirarin cewa ya ba wa jigon na jam’iyyar APC damar tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa a 2007, inda ya ce da gaske Tinubu ne ya nemi hakan, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku Tantirin Maƙaryaci Ne, In Ji Tinubu, Ya Tona Abin Da Ya Faru Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi a 2007

Atiku ya caccaki Tinubu
Zabo abokin gami Musulmi: Kwakwalwarsa ba ta aiki, Atiku ya caccaki Tinubu | Hoto: naijaonpoint.com.ng
Asali: UGC

Tinubu ya mayar da martani ga ikirarin Atiku a takarar shugaban kasa na 2007

Atiku, a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli a gidan talabijin na Arise, ya yi ikirarin cewa Tinubu ya nemi ya yi takarar mataimakinsa a karkashin jam’iyyar Action Congress, tare dashi amma ya ki amincewa saboda ganin hakan ya saba tsarin siyasar addini.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A martaninsa, Tinubu ya zargi Atiku da tafka karya, inda ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ne ya nemi ya ba shi mukamin.

Atiku ya ce kwakwalwar Tinubu ta samu matsala

Atiku, a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe ya fitar, ya bayyana cewa, ba wai karya kawai Tinubu ya tafka ba, akwai alamu ya gaza tunawa.

A cewar sanarwar:

Kara karanta wannan

Fasto Tunde Bakare Yayi Bayani akan goyon Bayan Tinubu da Sukar Kungiyar CAN Da aka Ce Yayi

“Ba za mu ce Bola Tinubu ya yi karya ba. Maimakon haka, muradinmu ne mu ba shi uzuri kuma mu dauka cewa kwakwalwarsa ba ta nan kamar yadda take a da.”

Sanarwar ta kara da cewa majiyoyi da dama sun tabbatar da batun Atiku a kan Tinubu, wanda ke nuna wasu halaye sababbi, haka nan jaridar This Day ma ta ruwaito.

‘Dan Majalisar da ke wakiltar yankin Atiku Abubakar ya tsere zuwa jam’iyyar NNPP

A wani labarin, a yammacin Talata, 5 ga watan Yuli 2022, labari ya zo mana daga hukumar dillacin labarai na kasa cewa Hammatukur Yattasuri ya bar PDP.

Honarabul Hammatukur Yattasuri wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Adamawa ya fice daga jam’iyyar PDP mai mulkin Adamawa.

Da yake jawabi a wajen wani taro a garin Yola, ‘dan majalisar ya ce ya fita daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP ne domin ya iya taimakawa al’ummarsa da kyau.

Kara karanta wannan

2023: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Kan 'Fastocin Bogi'

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.