Fasto Tunde Bakare Ya Musanta zargin sukar kungiyar CAN da Marawa Takarar Tinubu baya

Fasto Tunde Bakare Ya Musanta zargin sukar kungiyar CAN da Marawa Takarar Tinubu baya

  • Fasto Tunde Bakare ya karyata zargin da ake masa na cewa yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu
  • An zargi Fasto Tunde Bakare da cewa kungiyar CAN yan siyasa ne masu halin yan jam'iyyar PDP
  • Tunde Bakare ya ce gurbatattun marubata soshiyal midiya dake son bata mishi sunna ke yada labarun karya akan shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ogin - Fasto Tunde Bakare, ya musanta zargin da ake masa na cewa yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu. Rahtoton Channels TV

Bakare ya kuma karyata zargin da ake masa na cewa ya soki kungiyar kiristocin Najeriya dan adawar da suka nuna wa jami’iyyar APC akan kaddamar da takarar tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Kan 'Fastocin Bogi'

Martanin Fasto Bakare, ya zo ne a wani jawabi da ya fitar a ranar Juma’a inda ya karyata kalaman da aka ce shi yayi su.

Bakare ya ce marubuta marasa gaskiya a soshiyal midiya suka yi dan bata sunan shi.

Tinubu
Fasto Tunde Bakare ya Musanta zargin sukar kungiyar CAN da Marawa Tinubu baya FOTO PUNCH
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fasto Bakare ya ce:

“An zarge ni da cewa tada jijiyar wuya da kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN keyi dabara ce na tilasta wa APC daukan dan takara mai rauni.
“Kuma an zarge ni da cewa Kiristoci adalai ne masu hali irin na Yesu Kristi, amma yan kungiyar CAN ’yan siyasa ne masu halin PDP.
"Sai kuma karyar da aka watsa na cewa Tinubu ne dan takara na.
“Shin wannan ba shine Tinubu da na sanar da kowa da kowa ba a taron fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC da ba zan janye masa ba?

Kara karanta wannan

Atiku: Sowore Bai San Komai Ba Game Da Najeriya

Faston ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da wadannan kalamai da ake zargin shi yayi su.

Zabe 2023 : Bamu da matsala da zaben Kashim Shettima - Gwamnonin APC

A wani labari kuma, Gwamnoni Jami’iyyar APC na Arewa sun karyata zargin da ake musu na cewa daukar Kashim Shetiima da Tinubu yayi a matsayin abokin takarar sa na zabne 2023 bai musu dadi ba. Rahoton BBC

Gwamnonin sun ce suna goyon zabin da aka yi wa Kashim Shettima dari bisa dari saboda shi ma tsohon gwamna ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel