Tsoron Tinubu Da Shettima Yasa Yan Adawa Ke Babatu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Kungiya

Tsoron Tinubu Da Shettima Yasa Yan Adawa Ke Babatu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Kungiya

  • Kungiyar goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, TSO, ta ce tsoron Tinubu da Kashim Shettima ne yasa yan adawa suka fara babatu kan batun takarar musulmi da musulmi
  • Mallam Abdulazeez Yinka Oniyagi, jagoran kungiyar ta TSO ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi a Jihar Kwara yana mai cewa za su shirya tattaki na mutum miliyan daya domin Tinubu
  • Hon Aminu Suleiman, Direktan Kungiyar TSO na kasa ya ce da farko babu wanda ya yi batun tikitin musulmi da musulmi lokacin da Tinubu ya zabi Masari matsayin mataimaki har sai da ya zabi Shettima don suna tsoronsa shima

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kwara - Mallam Abdulazeez Yinka Oniyagi, Jagoran Kungiyar Goyon Bayan Tinubu (TSO) ya ce tsoron Tinubu da Shettima ne yasa masu adawa ke daukan nauyin masu dumama siyasa kan batun tikitin musulmi da musulmi.

Kara karanta wannan

2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN

Hakan ne zuwa ne a lokacin da Direkta Janar na TSO, Hon Aminu Suleiman ya ce kungiyar za ta koma ta yi nazari don kaucewa 'kuskuren' da jam'iyyar ta yi a Jihar Osun ranar Asabar.

Tinubu da Shettima.
Tsoron Tinubu Da Shettima Yasa Yan Adawa Ke Babatu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Kungiyar Goyon Baya. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Ya kara nuna gamsuwa cewa Asiwaju Bola Tinubu shine zai yi nasara a zaben 2023 duk da kayen da APC ta sha a Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dukkansu sun yi magana na a Jihar Kwara, yayin da suke bada alamun cewa za su shirya tattaki na mutane miliyan 1 domin dan takarar na APC.

Za mu koma teburin nazari don kada mu maimaita kuskuren da ya faru a Osun, Suleiman

Gwamna Adegboyega Oyetola na APC ya sha kaye a hannun dan takarar PDP Ademola Adeleke inda ya samu kuri'u 403,371 gwamnan mai ci kuma ya samu 375,027.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya yi ganawar sirri da fitaccen fasto kan batun Shettima

A cewar Suleiman, "Za mu koma allon zane mu ga gyare-gyaren da za mu yi don tabbatar da cewa ba mu maimaita kuskuren da ya faru ba."

A bangarensa, Oniyangi ya ce Tinubu ya shiga takarar da ayyukan da ya yi lokacin yana gwamnan Jihar Legas kuma labarin bata canja ba.

"Lokacin da ya nada Masari a matsayin mataimaki, babu wanda ya ce komai amma da ya karo Shettima wanda barazana ne ga yan adawa, labarin ya canja," ya kara da cewa.

Tsohon Shugaban Kungiyar Kirstocin Najeriya, CAN, Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamna a Najeriya

A wani rahoton, kun ji an zabi tsohon shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, a Jihar Kwara, Rabaran Joshua Olakunle, a matsayin dan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben 2023, rahoton This Day.

Rabaran Olakunle wanda ya fito daga Ora a karamar hukumar Ifelodun, zai yi takara ne tare da Mr Hakeem Oladimeji Lawal, wanda ya yi nasarar zama dan takarar jam'iyyar a zaben cikin gida na ranar 31 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel