Ba za mu sake yiwa Tinubu kamfen ba saboda zabar Musulmi da ya yi, Kiristocin APC a arewa

Ba za mu sake yiwa Tinubu kamfen ba saboda zabar Musulmi da ya yi, Kiristocin APC a arewa

  • Shugabannin kiristoci na ci gaba da watsi da tikitin Musulmi da Musulmi na Tinubu da Shettima gabannin zaben 2023
  • A yanzu haka kiristocin jam’iyyar APC a arewa sun yi watsi da zabar Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa
  • Kiristocin sun bayyana cewa ba za su iya zuwa mazabansu su tallata tikitin Musulmi da Musulmi ba

Shugabannin kiristoci na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a arewa sun bayyana cewa ba za su iya yiwa jam’iyyar kamfen ba saboda tsayar da Musulmi da Musulmi da aka yi a matsayin yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa. Nigerian Tribune ta rahoto.

A ranar Lahadi ne dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya bayyana Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zaben 2023. Hakan ya haifar da cece-kuce daga kungiyoyi daban-daban a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun jinjinawa APC da Tinubu kan zabar Shettima

A cikin wata takarda da suka saki bayan wani taro a ranar Litinin, shugabannin Kirista a fadin jihohin arewa 19 sun yi bore kan tikitin Musulmi da Musulmi na APC. Wasu ‘ya’yan jam’iyyar ma sun yi murabus kan wannan al’amari.

Tinubu da Shettima
Ba za mu sake yiwa Tinubu kamfen ba saboda zabar Musulmi da ya yi, Kiristocin APC a arewa Hoto: @HoeGee_Tyla
Asali: Twitter

Sun yi gargadi cewa idan har ba a janye batun zabar Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ba kafin 15 ga watan Yuli, toh za a samu gagarumin matsala, jaridar Vanguard ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Najeriya kasa ce mai addinai da dama da kuma kundin tsari na damokradiyya, kuma yin kutse a tsarin zai iya shafar zaman lafiya da ke wanzuwa a tsakanin al’umma.

A cewar takardar wacce Doknan Sheni, Ishaya Bauka da Saidu Ibrahim, Shugabannin kiristocin APC a Arewa suka sanyawa hannu, sun ce yanayin siyasar kasar a yanzu ya sha banban da abun da yake a 1993 lokacin da MKO Abiola wanda ya kasance Musulmi ya zabi dan uwansa Musulmi a matsayin abokin takara.

Kara karanta wannan

Don Tinubu ya zabi Musulmi: Jarumin Nollywood Kenneth Okonkwo ya fice daga APC

Sun kuma ce tikitin Musulmi da Musulmi sai sa mutane su ki yarda cewa jam’iyyar ba ta da ajandar Musulunci.

Wani bangare na jawabin ya ce:

“Yan siyasar APC kiristoci a jihohin arewa 19 sun gana a Abuja don tattauna lamarin yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa Musulmi da Musulmi na jam’iyyar da kuma illar hakan ga kasar.
“Taron ya yanke hukunci kamar haka: A matsayinmu na kiristoci a APC, zukatanmu da addininmu ba za su bamu damar zuwa mazabunmu daban-daban don yiwa Musulmi da Musulmi kamfen ba.
"Zabar Musulmi a matsayin abokin takara ya nuna rashin kishi ga kiristoci a kasar.
"Tsoron Kiristoci a arewa da ma kasar baki daya shine cewa za a dunga kallon APC a matsayin jam'iyyar Musulunci kuma cewa tikitin Musulmi da Musulmi bai yiwu ba a 2015, me zai sa shi yiwuwa a 2023?
“Bugu da kari, muna fargabar cewa wanda aka zabo yana da hannu a cikin ayyukan ‘yan matan Chibok da sauran ayyukan ta’addanci.

Kara karanta wannan

Tikitin Tinubu da Shettima mabudin nasara ne ga jam'iyyar APC, gwamna Buni

"Tikitin Musulmi da Musulmi zai kawo cikas ga zaben ‘yan takarar APC Kiristoci a jihohin arewa."

Kungiyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shigo lamarin don ra’ayin zaman lafiya da daidaituwar kasar.

Tikitin Tinubu/Shettima: Adamu Garba ya sake komawa jam’iyyar APC

A wani labarin kuma, mun ji cewa shahararren dan siyasa Adamu Garba ya sake komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya sauya sheka zuwa Young Progressives Party (YPP).

Garba ya bar jam’iyya mai mulki don yin takarar tikitin shugaban kasa a jam’iyyar YPP, amma sai ya sha kaye a hannun Malik Ado-Ibrahim.

Da ya mallaki fom din takarar shugaban kasa na YPP a watan Mayu, Garba ya ce matasa basu da makoma a jam’iyyar APC da Peoples Democratic Party (PDP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel