Tikitin Tinubu da Shettima mabudin nasara ne ga jam'iyyar APC, gwamna Buni

Tikitin Tinubu da Shettima mabudin nasara ne ga jam'iyyar APC, gwamna Buni

  • Tsohon shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya yabawa dan takarar shugaban kasa, Bola bisa zabar Shettima a matsayin mataimakinsa
  • Gwamnan na jihar Yobe ya bayyana cewa tikitin takarar musulmi da musulmi zai karawa jam’iyyar karfi gabanin zaben 2023
  • Buni ya ci gaba da cewa, Tinubu da Shettima na da hakuri da bin addini kuma sun dade suna aiki tare da zama tare mutane masu mabambantan addinai

Gwamna Mai Buni na jihar Yobe ya yabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, bisa zabin abokin takararsa, Kashim Shettima.

Kamar yadda Punch ya ruwaito, Buni, tsohon shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, ya bayyana Shettima a matsayin wanda ya cancanta yayin da ya bayyana matakin a matsayin tikitin samun nasara ga jam'iyyar.

Martanin Buni kan zabo Shettima
Tikitin Tinubu da Shettima mabudin nasara ne ga jam'iyyar APC, gwamna Buni | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Tikitin Tinubu da Shettima zai karawa APC karfi gabanun 2023, inji Buni

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan ganawa da Buhari, gwamnonin APC sun fadi matsayarsu kan takarar Tinubu da Shettima

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed, gwamnan ya bayyana cewa matakin zai kara fadada jam’iyyar da kuma kara mata damar samun nasara a zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani bangare na kalaman nasa ya ce:

“Hadakar Tinubu da Shettima ya sa jam’iyyar ta kara kwarin gwiwar tunkarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa tare da hango nasara a sarari."

Buni ya kara da cewa dan takarar shugaban kasan da mataimakinsa na jam’iyya mai mulki mutane ne masu albarka da kyawawan gogewa wajen gudanar da mulki.

Jigon na jam’iyyar ta APC ya ba da misali da irin gogewar da suka samu ta shugabanci, da kwarewa da kuma nasarorin da suka samu, wadanda suka zama musu shiri ga shugabancin kasar nan.

Kara karanta wannan

Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima

Sai dai ya ci gaba da cewa Najeriya na bukatar kyakkyawar gudunmawarsu da gogewarsu domin a halin yanzu tattalin arzikin duniya ke ciki a yanzu.

Ku hada kai, ku maida hankali nan da 2023, Buni ga APC

Gwamna Buni ya bukaci jam’iyyar da ta ci gaba da kasancewa kan ta a hade tare da mayar da hankalinta wajen samun nasara a zaben 2023.

Buni ya bayyana Tinubu da Shettima a matsayin mutane masu son addini, masu hakuri, aiki tukuru da zama da mutane daga addinai daban-daban.

Gwamna Buni ya ce:

“Jam’iyyar APC mai adadin mambobi sama da miliyan 40, da yardar Allah za ta lashe zaben 2023 bisa gaskiya da adalci.

Bayan ganawa da Buhari, gwamnonin APC sun fadi matsayarsu kan takarar Tinubu da Shettima

A wani labarin, Gwamnonin jam’iyyar APC tara sun yi ganawar sirri ta sa’a daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya gamsu da hadin Tinubu da Shettima

A karshen taron, gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar maaimakin shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, inji rahoton jaridar Punch.

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnonin sun kuma ce sun amince da hadakar Tinubu da Shettima domin tabbatar da nasarar jam’iyyar mai mulki a zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel