Osun: Jam'iyyun APC da PDP ba su da abun da zasu nuna, ku zaɓi NNPP, Kwankwaso

Osun: Jam'iyyun APC da PDP ba su da abun da zasu nuna, ku zaɓi NNPP, Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace manyan Jam'iyyun siyasa biyu ba su da bakin magana
  • Ɗan takarar shugaban kasan ya yi kira ga masoyansa na Osun su kakkaɓe katin zaben su, su zaɓi ɗan takarar NNPP
  • Kwankwaso wanda ya je Osun domin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar jam'iyyarsa a zaɓen 16 ga watan Yuli

Osun - Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyya mai kayan marmari, Rabiu Kwankwaso, ya ce jam'iyyar APC mai mulki da PDP duk sun gaza, don haka ya yi kira ga masu katin zaɓe su kaɗa wa NNPP kuri'unsu a zaɓen Osun da ke tafe.

Kwankwaso, wanda ya je Osun domin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan na jam'iyyarsa, ya roki mazauna jihar su fito kwansu da kwarkwata su kaɗa wa NNPP kuri'un su a ranar 16 ga watan Yuli, 2022.

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Rikicin PDP ya tsananta, Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamna a 2023

Sanata Rabiu Mus Kwankwaso.
Osun: Jam'iyyun APC da PDP ba su da abun da zasu nuna, ku zaɓi NNPP, Kwankwaso Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewarsa, shirin jam'iyyarsa na karɓan Najeriya a 2023 daga jihar Osun ya kamata ya fara tura alamu domin manyan jam'iyyu biyu ba su da ta cewa ga al'umma, jaridar Punch ta rahoto.

Tsohon gwamnan Kanon ya ayyana cewa kowane masoyinsa da ke zaune a jihar ya kakkaɓe katinsa ya shirya danna wa ɗan takarar gwamnan na NNPP kuri'arsa a zaɓe mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso ya yi wannan jawabi ne a Osogbo yayin wani taro da NNPP ta shirya domin nuna goyon baya ga ɗan takararta na gwamnan Osun, Dakta Oyelami Saliu.

Duk mara katin zaɓe ya garzaya ya mallaka - Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban kasan ya roki masu kaɗa kuri'a da suka yi rijistar katin zaɓe kuma ba su karɓo ba su garzaya su amso, sannan su tallafa wa jam'iyya a zaɓe.

A jawabinsa ya ce:

Kara karanta wannan

'Ba zamu duƙa mu roki Wike ba' Saɓani ya kunno kai a PDP kan zuwa a rarrashi gwamnan Ribas

"Dandazon mambobin jam'iyyar mu sun shirya kaɗa wa ɗan takarar mu kuri'un su. Alamar jam'iyyar mu ta yi ƙaurin suna kowa ya santa kuma tana nuna Najeriya a karkashinta zata dunƙule."
"Duk wanda bai karɓo katin zaɓen sa ba ya maza-maza ya karbo kuma ya danna wa jam'iyyar mu. Gaza zaɓen jam'iyyar mu da zata kawo canji mai amfani na nufin waɗan can mutanen su cigaba da tafiyar da harkokin ƙasar mu a kowane mataki."

A wani labarin kuma Rikicin jam'iyyar PDP ya tsananta, Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamna a 2023

Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke tikitin ɗan takarar da PDP ta tsayar a zaɓen gwamnan jihar Delta 2023.

Alkalin Kotun, Mai shari'a Taiwo Taiwo, ya ce hujjoji masu ƙarfi sun tabbatar da cewa Sheriff Oborevwori, bai cancanta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel