Jerin tsofaffin Gwamnonin jihohi 28 da za a iya gani a zauren Majalisar Dattawa a 2023

Jerin tsofaffin Gwamnonin jihohi 28 da za a iya gani a zauren Majalisar Dattawa a 2023

  • Akwai Gwamnoni masu-ci da-dama da ake tunanin za su zama Sanatoci a Majalisar Dattawa a zaben 2023
  • Wadannan Gwamnonin jihohi za su hadu da wasu tsofaffin Gwamnonin Najeriya da yanzu suke Majalisa
  • Idan Gwamnonin sun samu yadda suke so, za a cika Majalisar Dattawa da mutum 28 da sun taba rike Jihohinsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jaridar Premium Times ta kawo wani dogon rahoto da ya bayyana cewa majalisar dattawan kasar nan ta zama matattarar tsohon Gwamna.

A halin yanzu akwai tsofaffin gwamnoni 14 daga Kudu da Arewacin Najeriya da ke rike da kujerar Sanatoci, Wasu gwamnoni masu-ci kuma su na harama.

Akwai tsofaffin Gwamnonin da yanzu Sanatoci ne da suka rasa takara, a dalilin haka ne suka sauya-sheka, irinsu Ibrahim Shekarau da Adamu Aleiro.

A zaben 2023, zai yiwu a samu tsofaffin gwamnoni 28 da wadanda wa’adinsu zai kare a 29 ga watan Mayu da za a rantsar a matsayin Sanatoci a majalisa.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Sababbin shiga

Rahoton ya ce tsofaffin gwamnonin da yanzu su ke harin zama Sanatoci a kasar sun hada da:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majalisar Dattawa
Sanatoci a Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: UGC

1. Adams Oshiomhole

2. Dave Umahi

3. Aminu Tambuwal

4. Darius Ishaku

5. Samuel Ortom

6. Okezie Ikpeazu

7. Abubakar Sani Bello

8. Ibrahim Danwkambo

9. Abdulaziz Yari

10. Ifeanyi Ugwuanyi

11. Simon Lalong

12. Gbenga Daniel

Tsofaffin hannu

Jaridar ta ce tsofaffin Gwamnonin da suke kokarin zarcewa a kujerar majalisar dattawa:

13. Aliyu Wammako

14. Kabiru Gaya

15. Chimaroke Nnamani

16. Umar Al-makura

17. Danjuma Goje

18. Orji Kalu

19. Kashim Shettima

20. Ibrahim Gaidam

21. Seriake Dickson

22. Saminu Turaki

23. Gabriel Suswan

24. Ibrahim Shekarau

25. Adamu Aliero

26. Sam Egwu

27. Atiku Bagudu

28. Godswill Akpabio

Abin ya zama al'ada

Wani rahoto da mu ka fitar kwanakin baya, ya nuna cewa yanzu haka akwai tsofaffin gwamnoni fiye da 15 da su ke rike da kujera majalisar dattawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Dattijon Arewa ya soki Atiku da Tinubu, ya yabi Obi da Kwankwaso

A zaben da za ayi a 2023, akwai wasu gwamnoni da wa’adinsu zai kare da za su yi takarar Sanata. Za a samu wannan a Sokoto, Benuwai, Filato da watakila Ebonyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel