Jerin Gwamnoni 7 da ke kammala wa’adinsu a 2023 masu harin tafiya Majalisar Dattawa

Jerin Gwamnoni 7 da ke kammala wa’adinsu a 2023 masu harin tafiya Majalisar Dattawa

  • Ya zama tarbiyyar gwamnoni su yi ritaya a majalisar dattawa idan sun gama mulki a jihohinsu
  • A zaben da za ayi a 2023, akwai wasu gwamnoni da wa’adinsu zai kare da za su yi takarar Sanata
  • Yanzu haka akwai tsofaffin gwamnoni fiye da 15 da su ke rike da kujera majalisar dattawa a Najeriya

Daily Trust ta kawo jerin wasu daga cikin gwamnonin yau da ke neman zama Sanatocin gobe. A jerin akwai gwamnonin da ke mulki a APC da kuma PDP.

1. Simon Bako Lalong

Rahoton ya ce Gwamnan Filato, Simon Bako Lalong shi ne gwamnan da ya fara sayen fam din Sanata, zai kara da Nora Ladi Daduut a Filato ta Kudu a 2023.

Sanata Nora Ladi Daduut ta dare kujerar ne bayan mutuwar Sanata Ignatius Longjan a 2021. Kwamishinonin Filato ne suka hadawa gwamnan kudin fam.

Kara karanta wannan

Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

2. Muhammad Badaru Abubakar

Idan wa’adin Muhammad Badaru Abubakar ya cika a 2023, zai so ya zama ‘dan majalisar dattawa. Idan hakan ta tabbata, zai canji Sanata Abdullahi Danladi Sankara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Samuel Ortom

Gwamna Samuel Ortom ya shaidawa Duniya cewa zai yi takarar kujerar Sanatan Arewa maso yammacin Benuwai a 2023, zai kara ne da Emmanuel Orker Jev.

Kwanaki aka ji wasu dattawan jihar Benuwai sun hada kudi sun sayawa gwamnan fam a PDP.

4. Ifeanyi Okowa

Idan ya gama mulkin jihar Delta a Mayun 2023, Sanata Ifenayi Okowa yana da niyyar komawa kan kujerar Delta ta Arewa da ya bari a majalisar dattawa a PDP.

Wannan ya sa Sanata Peter Nwaoboshi ya koma APC domin ya iya zarcewa a kan kujerarsa.

Jerin Gwamnonin kudu
Gwamnonin Kudancin Najeriya a taro Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

5. Ifeanyi Ugwuanyi

Sanata Chukwuka Utazi bai da niyyar zarcewa a kujerar Enugu ta Arewa. Hakan yana nufin Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi zai nemi takarar majalisar dattawa a PDP.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Sanata Hayatu Gwarzo, ya zama mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewa maso Yamma

6. Darius Dickson Ishaku

Kamar a jihar Delta, a Taraba ma Gwamna Darius Ishaku yana so ya canji Emmanuel Bwacha a majalisar dattawa. Gwamnan zai nemi kujerar Sanatan kudancin Taraba.

7. Aminu Tambuwal

Duk da bai saye fam ba, ana tunanin Gwamna Aminu Tambuwal zai canji takarar Aminu Bala Bodinga idan har bai yi nasarar samun takarar shugaban kasa a PDP ba.

Umahi zai tafi Majalisa?

Daga cikin sauran gwamnonin da ake tunani za su iya karewa a majalisar dattawa a 2023 akwai David Umahi wanda yanzu haka zai yi takarar shugaban kasa a APC.

Amma kwanakin baya aka ji Francis Nwaze wanda ya na cikin masu magana da yawun Gwamnan, ya yi watsi da jita-jitar cewa zai hakura da shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel