Jerin manya 6 da suka yi wa Peter Obi mugun baki, su ka ce ba zai mulki Najeriya a 2023 ba

Jerin manya 6 da suka yi wa Peter Obi mugun baki, su ka ce ba zai mulki Najeriya a 2023 ba

  • Akwai mutanen da suka fito karara su na nuna takarar Peter Obi a zaben 2023 ba za ta je ko ina ba
  • Daga cikin wadanda suka ce ‘dan takaran na Labour Party (LP) ba zai ci zabe ba akwai Gwamnoni
  • Haka zalika Fasto Ejike Mbaka ya na ganin ba za a zabi Peter Obi ba saboda yana da ‘dan karen rowa

Nigeria - Jaridar nan ta The Nation ta kawo jerin ‘yan siyasa, masu mulki da shahararrun mutanen da suke da ra’ayin Peter Obi ba zai ci zabe a 2023 ba.

Ga jerin wadanda suke neman kashewa ‘dan takaran na Jam’iyyar Labour Party (LP) tun a yanzu:

1. David Umahi

Kwanakin baya an ji Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi yana cewa mutanensa ba za su zabi jam’iyyar Labour Party ba, a cewarsa APC za ta ci zabe.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

An rahoto David Umahi yana wannan bayani ne a lokacin da ya rantsar da wasu sababbin kwamishinoni da hadimai a gidan gwamnati a Abakaliki.

2. Muazu Babangida Aliyu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka yi hira da tsohon gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu, ya nuna mutanen Najeriya ba su shirya zaben Peter Obi a shekara mai zuwa ba.

Dr. Muazu Babangida Aliyu ya shaidawa Channels TV cewa Obi zai sha kasa a zaben 2023, sai dai watakila zai iya kai labari a zaben 2027 ko kuma 2031.

3. Ejike Mbaka

A baya an ji yadda Faston cocin AMEN da ke jihar Enugu, Ejike Mbaka, ya ke cewa tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi mutum ne mai rowa.

Ejike Mbaka wanda tun kafin a je ko ina ya gano Goodluck Jonathan zai fadi zaben 2015 yace Obi wahalar banza kurum zai yi domin sam ba zai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shahararren 'Dan kasuwan Najeriya ya ba takarar Peter Obi kwarin gwiwa

Peter Obi
Peter Obi da Pat Utomi Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

4. Ned Nwoko

Sanatan PDP na shiyyar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, Prince Ned Nwoko, ya ce Peter Obi ba zai iya lashe zaben shugaban kasa karkashin jam’iyyar LP ba.

An ji Hon. Ned Nwoko yana mai cewa zai fi kyau Obi ya dawo PDP domin ya samu kujerar Minista, ganin jam’iyyar adawar ba ta da karfin lashe zaben kasa.

5. Ike Ekweremadu

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya ce ba zai yiwu Peter Obi ya yi galaba a zaben shugaban kasa a jam’iyyar LP ba.

An ji Ike Ekweremadu yana cewa babu yadda Labor Party za ta kafa gwamnati domin kuwa mutanen kudu maso gabas za su zabi PDP ne a zaben 2023.

6. Yakubu Ajaka

Da aka tambayi Yakubu Ajaka game da makomar Peter Obi da Atiku Abubakar, sai ya nuna cewa idan an buga gangar siyasar 2023, mutane za su gane zahiri.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Yajin-aikin Kungiyar ASUU ya kusa zama tsohon labari - Gwamnatin Buhari

Mataimakin sakataren yada labaran na APC ya ce ana zuga tsohon gwamnan na Anambra ne a kafofin sada zumunta na zamani, amma ba zai je ko ina ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel