Daga karshe: Ta karewa Ahmad Lawan, INEC ta ce Machina ya lashe zaben fidda gwani

Daga karshe: Ta karewa Ahmad Lawan, INEC ta ce Machina ya lashe zaben fidda gwani

  • Daga karshe dai INEC ta fitar da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan daga jerin 'yan takarar sanata na APC a Yobe a 2023
  • Hukumar zabe a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni, ta fitar da kwafin gaskiya na zaben fidda gwanin sanata na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayu
  • Wannan takarda da INEC ta fitar ta amince da Bashir Sheriff Machina a matsayin dan takarar jam’iyya mai mulki na gaskiya a kujerar sanata a Yobe

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi watsi da batun zabo shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a zaben fidda gwani na sanatan Yobe ta Arewa.

A maimakon haka, hukumar ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin dan takara na gaskiya a jam’iyyar APC a jihar ta Arewa maso Gabas, inji rahoton PM News.

Kara karanta wannan

APC ta kawo karshen rigimar cikin gidan da aka yi shekaru 8 a jere ana gwabzawa

Ta karewa Ahmad Lawan a zaben 2023
Ta karewa Ahmad Lawan, INEC ta amince Machina ya yi takarar sanata | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Wani tabbataccen kwafin rahoton INEC daga zaben da aka gudanar ya nuna cewa Machina ya samu kuri’u 289 cikin 300 da deliget suka kada.

Rahoton ya tabbatar da ikirarin da Machina ya yi tun farko a bainar jama'a cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwanin da aka yi kuma ya lashe tikitin takara gabanin babban zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Takardar da INEC ta tabbatar a ranar 23 ga watan Yuni, 2022, ta amince da takarar Machina kuma ta yi shiru gaba daya game da sunan Sanata Lawan a cikin 'yan takara, Gazette Nigeria ta ruwaito.

Lawan ya tsallake rijiya da baya, sunansa ya maye gurbin na Machina a matsayin dan takarar sanata na APC

A wani labarin, an bayyana sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yobe North: Abin Da Yasa Muka Tura Wa INEC Sunan Ahmad Lawan, Shugaban APC, Adamu

Lamarin na zuwa ne yan awanni bayan Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar, ya jadadda cewa ba zai janyewa shugaban majalisar dattawan ba.

Lawan dai ya yi takarar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar APC sannan awanni kafin fara zaben fidda gwanin sai shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sanar da shi a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel