Daga karshe, Sanata Okorocha ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaɓen fiida gwanin APC

Daga karshe, Sanata Okorocha ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaɓen fiida gwanin APC

  • Bayan kwanaki aƙalla biyar da shan kaye, Sanata Rochas Okorocha ya tura sakon murna ga tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu
  • Sanata Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo ya ce yana wa jagoran APC na ƙasa fatan samun nasara a babban zaɓen 2023
  • Okorocha wanda bai samu kuri'a ko ɗaya a zaben fidda gwanin APC, ya yaba wa sauran abokanan takara

Abuja - Sanata mai wakiltar mazaɓar Imo ta yamma a majalisar dattawa, Sanata Rochas Okorocha, ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na APC.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Okorocha wanda ya na ɗaya daga cikin yan takara a APC, ya yi wa Tinubu fatan samun nasara a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Ko shi zai zama mataimaki? Bola Tinubu ya sa labule da wani gwamnan Arewa a Abuja

Bola Tinubu tare da Rochas Okorocha.
Daga karshe, Sanata Okorocha ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaɓen fiida gwanin APC Hoto: inlandtown.com
Asali: UGC

Haka zalika, Okorocha ya yaba wa sauran waɗan da suka fafata a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar da zai gaji Buhari a jam'iyyar APC.

A sakon taya murnan da ya saki a shafinsa na Facebook, Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina son miƙa sakon murna ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bisa nasarar da ya samu a zaɓen fitar da ɗan takarar na jam'iyyar mu, All Progressive Congress wato APC."
"Haka nan kuma ina son yi masa fatan samun nasara a babban zaɓen 2023 da ke tunkaro mu nan gaba kadan."
"Ina mai miƙa yabo da jinjina ga dukkan yan takara waɗan da suka fafata a zaɓen fidda gwani da nufin samun tikitin takarar shugaban ƙasa na APC."

Legit.ng Hausa ta ruwaito muku cewa Tinubu ya samu kuri'u 1,271 inda ya lallasa abokan takararsa na kusa, Rotimi Amaechi, da kuma mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Karon farko bayan lashe zaɓen APC, Tinubu ya lallaɓa ya sa labule da shugaban ƙasa

Yan takaran da suka fafata a zaɓen

Ya fafata da yan takara 13 da suka haɗa da, Chukwuemeka Nwajiuba, Fasto Tunde Bakare, Ahmed Rufai, Sanata Rochas Okorocha, Mista Jack Rich, Gwamna Ben Ayade, da gwamna David Umahi.

Sauran sune; Sanata Ahmed Yarima, Dakta Ahmed Lawan, Farfesa Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Gwamna Yahaya Bello da kuma Ogbonnaya Onu.

A wani labarin na daban kuma Wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya zabi wanda zai zama mataimakinsa a 2023

Yayin da manyan jam'iyyu ke ta faɗi tashin neman mataimaki,Farfesa Umeadi, ya kawo karshen kace-nace a jam'iyyar APGA.

Ɗan takarar da jam'iyyarsa sun amince Kwamaret Muhammed Koli ya zama mataimaki yayin zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel