El-Rufa'i: Buhari Ya Goyi Bayan Shawarar Da Muka Yanke Na Mayar Da Mulki Kudu a 2023

El-Rufa'i: Buhari Ya Goyi Bayan Shawarar Da Muka Yanke Na Mayar Da Mulki Kudu a 2023

  • Gwamna Nasir El-Rufai ya ce tunda farko Shugaba Muhammadu Buhari ya goyi bayan gwamnonin arewa da ke son mayar da mulki kudu a 2023
  • Gwamnan na Jihar Kaduna ya ce gwamnoni biyu ne kawai ba su amince da hakan ba; Gwamna Yahaya Bello na Kogi da Mai Mala Buni na Jihar Yobe
  • El-Rufai ya ce a yayin da suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari kan batun wanda ya ke son ya gaje shi, ya ce su kawo musu sunan mutum biyar amma cikinsu ya ce daya ne kadai zai iya jagorantar Najeriya

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dade yana goyon bayan matakin da gwamnonin arewa a APC suka dauka na mayar da mulki kudu a 2023.

Gwamnan na Jihar Kaduna ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels Television.

El-Rufai: Buhari Ya Goyi Bayan Shawarar Da Muka Yanke Da Mayar Da Mulki Kudu a 2023
Buhari Ya Goyi Bayan Shawarar Da Muka Yanke Da Mayar Da Mulki Kudu a 2023, El-Rufa'i. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Gwamnoni biyu kawai da ba su yarda da mu ba sune Yahaya Bello wanda ke takara da Mai Mala Buni wanda ke goyon bayan shugaban majalisar dattawa kuma muna ganin hakan ne alheri ga jam'iyyarmu, arewa da Najeriya don haka shugaban kasa ya bamu goyon baya dari bisa dari," in ji El-Rufai.

Ya kara da cewa bayan taron da suka yi suka cimma matsayar kuma takardar da ya kamata a mika wa Shugaba Buhari ta fito a kafafen watsa labarai, Gwamna El-Rufai ya ce shugaban kasar ya yi murnar yadda labarin ma ya fita.

Ya ce:

"Mun tura tawaga ta sanar da Shugaban Kasa matsayar mu amma kafin su samu ganinsa, takardar da muka rattaba hannu a kai ta fita kafafen watsa labarai, tawagar ba ta ji dadi ba kuma suka fasa ganin shugaban kasar.

"Bayan yan kwanaki, mun ga shugaban kasar, muka mas bayanin abin da ya faru har takardar ta fita ba da izinin mu ba.
"Baya ga jin dadin fitar takardar ta mu, shugaban kasar ya fada masa ba shi da wani dan takara da ya ke son ya gaje shi."

El-Rufai ya ce Buhari ya umurci gwamnonin arewan su gabatar masa da sunayen mutane biyar.

"Shugaban kasar ya fada mana mu tafi mu gana da jam'iyya, mu bashi sunan mutum biyar sai ya duba yiwuwar zaben daya cikinsu. Bayan kwana guda, mun mika masa sunayen, ya duba sai ya ce dukkansu yan kudu ne amma daya kadai zai iya shugabancin Najeriya, mu tafi zaben fidda gwani, Allah ya bawa wanda ya fi cancanta nasara," ya kara da cewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel