Zaben fidda gwanin APC: Jerin jihohin da Tinubu, Osinbajo da sauran yan takara za su iya lashewa

Zaben fidda gwanin APC: Jerin jihohin da Tinubu, Osinbajo da sauran yan takara za su iya lashewa

Wani rahoton nazari daga jaridar The Nation ya yi hasashen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya yi a ranar Talata, 7 ga watan Yuni, a Abuja.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A cewar rahoton, Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagas, yana da kwarjini, isa, tsari, goyon baya, farin jini, tarihin nasara, da kwarewar aiki sosai a bangarorin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Tinubu wanda ya kafa APC tare da shugaba Buhari da sauran masu ruwa da tsaki ya kuma horar da yan siyasa a fadin kasar nan, wanda da dama daga cikinsu suka zama gwamnoni, sanatoci, yan majalisar wakilai da sauransu.

Zaben fidda gwanin APC: Jerin jihohin da Tinubu, Osinbajo da sauran yan takara za su iya lashewa
Zaben fidda gwanin APC: Jerin jihohin da Tinubu, Osinbajo da sauran yan takara za su iya lashewa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

An kuma tattaro cewa jagoran na APC yana da goyon bayan yawancin gwamnoni fiye da abokan hamayyarsa. Wannan ya bashi fifiko kan sauran domin gwamnonin na da karfi sosai a kan deleget wadanda za su kada kuri’a a zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Ga adadin jihohin da ake sa ran Tinubu da sauran yan takara za su lashe:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asiwaju Bola Tinubu

 1. Kano
 2. Lagos
 3. Oyo
 4. Borno
 5. Sokoto
 6. Bauchi
 7. Osun
 8. Benue
 9. Ondo
 10. Edo
 11. Katsina
 12. Gombe
 13. Niger
 14. Kaduna
 15. Zamfara
 16. Adamawa

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo

 1. Ogun
 2. Nasarawa.

Yahaya Bello

 1. Kogi

Rotimi Amaechi

 1. Rivers
 2. Plateau

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan

 1. Yobe
 2. Kebbi (da karfi)
 3. Abia
 4. Imo
 5. Ebonyi
 6. Anambra
 7. Enugu

Kayode Fayemi

 1. Ekiti
 2. Jigawa
 3. Kebbi

Godswill Akpabio

 1. Akwa Ibom
 2. Ben Ayade
 3. Cross River

Jihohin da ba tabbass

 1. Delta
 2. Bayelsa

Zaben fidda gwanin APC: Akpabio ya yi zazzafan martani game da janyewa daga tseren shugabancin kasa

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

A wani labarin, daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ba zai janye daga tseren kujerar ba.

Hakan na zuwa ne yan awanni bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki sannan ya bukaci da su fito da dan takarar maslaha.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom, ya bayyana rade-radin cewa ya janye daga tseren a matsayin mugun karya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel